Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 20:38:29    
Jami'an kasashen Afrika, da jakadunsu da ke kasar Sin, da wakilai daga kungiyoyin kasashen duniya sun nuna juyayi ga mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasa na Wenchuan

cri
A gun taron karawa juna sani na bunkasuwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka da aka shirya a yau 20 ga wata a nan birnin Beijing, manyan jami'an gwamnatoci daga kasashe guda 17 na Afrika, da jakadu fiye da 10 na kasashen Afrika da ke nan kasar Sin, da kuma wakilai daga kugiyoyin kasashen duniya, sun nuna juyayi ga mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da aka samu a Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin.

Kafin taron, a karkashin shugabancin mai jagorancin taron, jami'an gwamnatocin kasashen Afrika, da wakilai daga hukumomin kasashen duniya, ciki har da bankin duniya, wadanda yawansu ya kai kusan 50, sun tashi tsaye don nuna ta'aziyya har na minti daya ga mutanen da suka mutu a sanadiyar girgizar kasa na Wenchuan.

A ranar 20 ga wata ne, aka bude taron karawa juna sani na bunkasuwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka a nan birnin Beijing, batutuwan da za a tattauna cikin taron su ne, yadda kasashen Afirka za su iya koyon ilmin bunkasa tattalin arziki daga kasar Sin. Manyan jami'ai daga kasashe 17 na Afirka, da kwararrun gida da na waje suna halartar taron. (Bilkisu)