Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 20:25:33    
An fara kai wadanda suka ji raunuka sakamakon girgizar kasa a lardin Sichuan zuwa birane da larduna daban daban na kasar Sin

cri
 

Domin samar da muhalli mai kyau ga mutanen da suka ji raunuka sakamakon girgizar kasar, a yayin da likitoci ke lura da wadanda ba su ji raunuka masu tsanani ba, suna kuma sanya ido a kan mutanen da suka ji raunuka masu tsanani cikin sa'o'i 24 kowace rana. Bisa kokarinsu, wasu masu raunuka da suka isa tun tuni sun fara samun lafiya. Mr.Hou Shunqi, wanda ya ji rauni, wanda ya zo daga garin Mianzhu, ya ce,"Muna fatan bisa kokarin likitoci, dukan mutanen da suka ji raunuka sakamakon girgizar kasar, za su warke su sami lafiya tun da wuri."

A halin yanzu dai, yawancin masu raunuka suna taruwa a wasu manyan asibitoci na birnin Chongqing. Ban da su kuma, wasu asibitoci kusan dari a unguwanni daban daban su ma a shirye suke. Shugaban sashen kiwon lafiya na birnin Chongqing, Mr.Qu Qian ya bayyana cewa,"A 'yan kwanaki masu zuwa, za a kai masu raunuka kusan 1500 zuwa birninmu, ya zuwa yanzu dai, asibitocin da za su karbe su sun riga sun share fage sosai."

Ban da birnin Chongqing, asibitocin da ke lardunan Shan'xi da Yunnan da Guizhou su ma za su karbi mutanen da suka ji raunuka sakamakon girgizar kasar. Ma'aikatar kiwon lafiya da ma'aikatar sufurin jiragen kasa na kasar Sin sun nemi asibitocin da abin ya shafa da su kafa sassan shugabanci na musamman da kuma kungiyoyin masana. Bayan haka, a yayin da ake jigilar masu raunuka, dole ne ma'aikatan jirgin kasa su kasance wadanda suka sami horaswa daga kungiyar Red Cross.

An ce, a halin yanzu, a kalla dai akwai masu raunuka dubu 20 da za a kai su zuwa biranen da ke waje da lardin Sichuan. Yau da kuma gobe, jiragen kasa kusan 10 za su isa lardin Sichuan bi da bi, don jigilar masu raunuka daga lardin Sichuan.(Lubabatu)


1 2