A ran 19 ga wata da yamma da misalin karfe 2 da minti 28, an ji karar jiniya da ta motoci da jiragen kasa a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin, dubban jama'a 'yan kabilu daban-daban wadanda suka je babban filin fadar Potala tun tuni sun yi tsit tare domin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.
Bayan da aka yi bikin nuna alhini, kuma mutane da yawa suna tsaye cik har dogon lokaci, ba su son tashi daga can. Ko ina ana iya ganin fararen hula suna yin sujada da huduba a gaban fadar Potala.
Daga karfe 2 da minti 31 na wannan rana da yamma, sufaye na dakin ibadan Jokhan sun fara yin addu'a , sufaye fiye da 90 wadanda ke sanye da manyan riguna masu launin ja suna yin huduba da murya daya cikin wani babban dakin yin addu'a, sun yi haka ne domin yin addu'a ga wadanda da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, da yin fatan alheri ga mutanen da suke da rai.
Bayan aukuwar babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, mutane 'yan kabilu daban-daban na jihar Tibet sun sha yin bukukuwan ba da kyautar kudi da samun karo-karon kudin da aka bayar domin nuna kauna ga mutane masu fama da bala'in girgizar kasa. (Umaru)
|