A ran 20 ga wata, kungiyar ceto ta maganin inganta tunani ta karo ta farko ta hukumar Redcross ta kasar Sin ta tashi daga birnin Beijing domin zuwa yankunan girgizar kasa a lardin Sichuan, za ta gudanar da aikin maganin inganta tunani, da horar da masu aikin sa kai a yankunan, domin kawar da illa daga babbar girgizar kasa tun da wuri, da kuma fara sabon zaman rayuwar jama'a.
Ana kyautata zaton cewa, kungiyar ceto ta maganin inganta tunani za ta shafe kwanaki 10 tana aiki a yankin Mianyang na lardin Sichuan. A ranar 21 ga wata, kungiyar Redcross ta kasar Sin za ta kara tura wata kungiyar maganin inganta tunani zuwa yankin Mianyang.
A ran 18 ga wata, a karo na farko ne, gidan rediyon kasar Sin, da kuma gidan redion tsakiya na jama'ar kasar Sin suka fara watsa wani shiri na maganin inganta tunani bayan faruwar girgizar kasa. Kwararru na gida da na waje za su yi amfani da wannan shiri cikin dogon lokaci, domin bayar da taimako ga jama'ar da ke fama da girgizar kasa wajen maganin inganta tunani.(Danladi)
|