Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 19:19:22    
Shugabanni na kasashe da yawa sun je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa

cri

A 'yan kwanakin baya, bi da bi ne, shugabanni na kasashe daban daban ciki har da Kodivwa, da Korea ta arewa, da Peru, da Ecuatorial Guinea, da Chile, da Lebanon da dai sauransu suka je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa.

A ran 19 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Kodivwa Mr. Youssouf Bakayoko ya je ofishin jakadancin kasar Sin da ke Kodivwa, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamkon babbar girgizar kasa da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.

Ban da shi kuma, shugabannin kasar Korea ta arewa, da na Mongolia, da mataimakin shugaba na farko na kasar Peru, da kuma firayin minista da kuma ministoci 10 na kasar, da firayin ministan kasar Ecuatorial Guinea, da shugabannin majalisun dattawa da wakilai, da ministan harkokin waje na kasar Lebanon su ma sun mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamkon babbar girgizar kasa.(Danladi)