Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:40:25    
Bangarorin daban daban na kasar Sin sun ci gaba da ba da kudi da kayayyakin agaji ga yankin bala'in girgizar kasa

cri

A cikin kwanakin nan, bangarorin daban daban na kasar Sin sun ci gaba da ba da kudi da kayayyakin agaji ga yankin bala'in girgizar kasa na gundunar Wenchuan ta jihar Sichuan.

A ran 19 ga wata da safe, an riga an yi jigilar kayayyakin agaji da ya kai kusan kudin RMB miliyan 10 da babbar kungiyar ma'aikatan kasar Sin suka saya zuwa yankin bala'in girgizar kasa. Ya zuwa ran nan da karfe 4 da yamma, jimlar kudin da kungiyoyin ma'aikatan kasar Sin da jama'a suka ba da ya kai kudin RMB miliyan 214.

Ya zuwa ran 19 ga wata da karfe 5 da yamma, bankin gine-gine na kasar Sin ya riga ya ba da kudin agaji da yawansa ya kai kudin RMB miliyan 70.26 ga yankin bala'in.

Ya zuwa ran 19 ga wata, yawan kudin agaji da gwamnatin yankin musamman na Macow da bangarorin daban daban suka ba da ya riga ya kai kudin Macow miliyan 120.

Yan uwa na Taiwan da kamfanoninsu dake jihar Fujian a kudu maso gabashin kasar Sin kuma sun ba da kudi da kayayyakin agaji da yawansu ya kai kudin RMB miliyan 40. (Zubairu)