Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:34:15    
Gamayar kasa da kasa sun yabawa aikin ceto don yaki da bala'in girgizar kasa da kasar Sin ke yi

cri

A ran 19 ga wata, wadansu shugabanin kasashen waje sun jajanta tare da nuna tausayi ga mutanen Sin masu fama da bala'in girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan a jihar Sichuan a kasar Sin, kuma sun yabawa aikin ceto na yaki da bala'in girgizar kasa da kasar Sin ke yi.

A ran 19 ga wata da safe, babban sakataren MDD Mr. Ban Ki-moon ya zo wurin zaunaniyar tawagar kasar Sin dake MDD don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon bala'in, ya yabawa kasar Sin sabo da karfi da kasar Sin ke nuna wa lokacin da take fuskantar kalubalen. Ya yi imani cewa, tilas ne mutanen kasar Sin su warware matsalar nan da suke fuskantar bisa jagorancin gwamnatin kasar Sin.

Ran nan kuma, shugaban kasar Botswana Mr. Ian Khama ya gana da jakadan kasar Sin dake kasar Botswana Mr. Ding Xiaowen don kara fahimtar halin da ake ciki game da bala'in girgizar kasa da ta auku a gundanar Wenchuan, inda ya ce, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da sauri sosai lokacin da suke fuskantar bala'in, bangarorin daban daban sun yi hadin gwiwa, aikin ceto yana tafiya cikin lami lafiya kuma ya samu babban ci gaba, wannan ya burge bangaren Botswana sosai.

Ministan harkokin waje na kasar Uganda Mr. Sam Kutesa ya je gidan jakadan kasar Sin dake kasar Uganda don nuna ta'aziya ga mutanen da suka mutu sakamakon bala'in girgizar kasa na gundunar Wenchuan, kuma ya yabawa kasar Sin sosai sabo da aikin ceto mai amfani da kasar Sin ke yi. Ya ce, bayan bala'in girgizar kasa ya auku, gwamnatin kasar Sin ta yi iyakancin kokarinta wajen ba da ceto ga wadanda suka ji rauni, an yabawa abin da take yi sosai. (Zubairu)