Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:32:12    
Gabobbin kogin Hai na birnin Tiang jin suna da ni'ima sosai

cri

Mun kai ku zuwa wani kauyen dake kusa da birnin Tiang jin, manoma na wannan kauye sun iya yin zane, har hotunnan da suka yi an sayar da su ne zuwa wurare daban daban na duk kasar Sin har zuwa kasahse da yawa a duk duniya. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ku zuwa wani shahararren kogi mai suna Hai he don gani kyakkyawan hali na gababbobin tekun nan dake cikin birnin Tiang jin.

Kogin Hai he yana ratsa birnin Tiang jin, ana kiran shi kogin mahaifa. Domin birnin Tiang jin ya samu bunkasuwa ne bisa albarkacin halittar kogin Hai he, ta haka ne kogin Hai he ya kawo zaman laheri ga jama'a na birnin Tiang jin. Mutane na birnin Tiang jin sukan dau kananan jiragen ruwa kan kogin nan, suna kallon kyakyawan halin kogi da wuri mai ni'ima sosai suna tafiya kan teku, Kai suna jin dadi sosai. Saboda kafin kasar Sin ta samu 'yancin kai, wurin nan da kananan ofisoshin jakadu na kasashen waje da kungiyoyin 'yan ciniki na duniya suka tattara a nan, Sabo da haka a kan tekun ana tafiya ana iya gani kyakkyawan halin gine gine iri iri da aka gina a gabobbin kogin nan, kuma sigogginsu Kaman na kasashen Turai. Yanzu, a birnin Tiang jin ana nan ana yin gine gine a shiyoyyi daban daban,daga cikinsu wadansu Kaman na kasar Faransa da na kasar Italiya da na kasar Rasha. Mr. Jing tie lin wani jami'I na ofishin kwamitin neman bunkasuwar ayyukan yawon shakatawa na birnin Tiang jin ya gaya wa wakilin rediyonmu cewa, bayan da shiyyar halin musamman ta Faransa ta kafu, gabobbin tekun Hai he za su kara kyakkyawan gani sosai, wato za su kara halin mumman nasu. Wannan jami'I ya ce, shiyyar halin musamman na kasar Farans tana da fadin hekta 600, cikin har da cibiyar yin nishadi, da lambun shan iska na irin kasar Faransa da gadojin da za a gina kan tekun nan iri na kasar Faransa.

A cikin 'yan shekaru da suka shige, gine gine na birnin Tiang jin sun samu bunkasuwa da sauri, ga manyan gine gine iri na zamani suna layi layi a gabobbin kogin nan, kai duk wannan yana ba da shaida cewa, birnin Tiang jin birni ne na zamani sosai, saboda haka ne masu yawon shakatawa su iya gani wadatuwa da zamani ke tasowa a birnin Tiang jin.

Da ake yin magana kan sauye sauye na birnin Tiang jin, sai mutane na birnin Taing jin ne suke iya sani sosai. Wani tsoho shi ne matukin karamin jirgin ruwa na da dake kan kogin Hai he, tsawon lokacin da yake tuka jirgin ruwa a kan wannan kogi yakai fiye da shekaru 30 da suka shige, saboda haka ne ya duba sauye sauyen da aka yi a bayane sosai. Ya gaya wa wakilin rediyon kasar Sin cewa, a shekara ta l970, na fara tuka karamin jirgin ruwa dake kan wannan kogi, na ga manyan sauye sauyen da aka yi a gabobbin wannan kogi, a da a gabobbin kogi babu babban ginin dake gabobin teku ko daya, wata gada daya dake kan wannan kogi ta lalace sosai, amma yanzu ga gadojji da yawa masu kyakkyawan gani da masu inganci da aka gina yanzu a kan kogin nan. Mutane na birnin Taing jin suna son yawon shakatawa a gabobbin kogin nan, in karshen mako ya zo, kai ga mutane da yawa sosai suna yawon suna shan nishadi a gabobbin kogin nan.

Wani jami'I na gwamnatin birnin Tiang jin ya gaya mana cewa,gwamnatin birnin Tiang jin ta sa rai sosai, tana yin kokarin don mai da kogin Hai he da ya zama shahararren kogi na duk duniya. Zuwa shekara ta 2005,bayan da an kammala gyare gyaren da za a yi, sai gabobbin kogin za su kara kyakkyawa, ba shakka zai iya jawo kyakkyawar damar yin yawon shakatawa sosai da sosai, zuwa wancan lokaci ne za a iya kara jawo masu yawon shakatawa na gida da na kasashen waje zuwa wurin nan.