Babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan wata makaranta ce ta musamman da aka kafa ta don 'yan makaranta na yankunan da ke kan duwatsu masu fama da talauci a birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin, haka kuma tana kasancewa da wani abin koyi da gwamnatin jihar Ningxia ta yi wajen neman samun ilmi cikin adalci. To, a cikin shirinmu na yau, za mu leka wannan makaranta.
An kafa babbar makarantar dutsen Liupan a shekara ta 2004, kuma gwamnatin jihar Ningxia ita ce ta samar da dukkan kudaden karatu da na wuraren kwana ga 'yan makaranta na gundumomi 9 masu fama da talauci, ban da wannan kuma ta samar da kudin Sin wato Yuan 1000 ga ko wanensu da suka zo daga kauyuka a ko wace shekara. Ya zuwa yanzu, 'yan makaranta kusan 3000 daga wadannan gundumomi 9 sun shiga makarantar, kuma kashi 40 bisa dari daga cikinsu su ne 'yan kabilar Hui, kashi 80 bisa dari daga cikinsu 'yan kauye ne.
Shugaban hukumar ilmi ta jihar Ningxia Cai Guoying ya bayyana cewa,
"A lokacin da, mun dauki dimbin matakai wajen warware matsalar fama da talauci, amma idan ana son warware matsalar kwata-kwata, to dole ne a kyautata ingancin mutane da na al'umma. Kuma mun kafa wannan makaranta ne domin 'yan makaranta na-gari da suka zo daga yankunan da ke kan duwatsu sun iya samun ilmi yadda ya kamata a yankuna masu ci gaba, ta haka za a iya cimma burin samar da taimako a fannonin basira da fasaha da kuma ilmi ga wurare masu fama da talauci. Haka kuma muna ganin cewa, muddin ta hanyar, za a iya warware matsalolin da yankuna masu fama da talauci suke fuskanta kwata-kwata."
Ma Sheng, wani dan makaranta ne da ya shiga babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan a shekarar da ta gabata, gidansa yana fama da talauci sosai, shi ya sa yana ganin cewa, ya yi sa'a da ya iya shiga makarantar. Kuma ya gaya mini cewa,
"a makarantar da na taba yin karatu a ciki, kayayyakin koyarwa ba kyau, kuma malamai ba su da kwarewa sosai wajen aiki. Amma wannan makaranta tana da matukar kyau, ana iya samun kayayyakin karatu na zamani. Ban da wannan kuma malamai suna lura da karatu da zaman rayuwarmu. Shi ya sa na girmama wannan kyakkyawan muhallin karatu sosai."
Ya zuwa yanzu, babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan ta riga ta zama daya daga cikin makarantun sakandare goma na jihar Ningxia da suke zama abubuwan koyi. A shekarar da ta gabata, 'yan makarantar na rukunin farko sun shiga jarrabawar neman shiga jami'a, kuma 414 daga cikin 604 sun ci jarrabawar. Haka kuma a shekarar nan da muke ciki, 'yan makaranta 745 daga cikin 1008 sun ci jarrabawar. Wang Yanning, wata 'yar makarantar dutsen Liupan, wadda za ta shiga jarrabawar neman shiga jami'a a shekara mai zuwa. Ta gaya mini cewa, ta yi limani da shiga jami'ar koyon ilmin yin cinikkaya tare da kasashen waje ta Beijing. Kuma ta kara da cewa,
"yankin da nake ciki yana da wuyar zuwa, kuma yana fama da talauci sosai. Sabo da haka ina jin murna kwarai da gaske da na samu wannan kyakkyawar damar karatu. Bayan da na samu ilmin cinikayya, zan komo gida don tallafa wa yankinmu wajen samun bunkasuwa."
Ganin saurin bunkasuwar babbar makarantar sakandare ta dutsen Liupan, shugaban hukumar ilmi ta jihar Ningxia Cai Guoying ya bayyana cewa, irin wannan gwaji na yin amfani da albarkatun birni wajen kafa makarantu don yaran da ke yankuna masu fama da talauci ya samu nasara sosai.(Kande Gao)
|