Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:22:37    
Kungiyoyin duniya da jakadun kasashe daban daban a Geneva sun nuna babban alhani ga wadanda suka mutu a sakamakon girgizar kasa a Sin

cri
Bisa sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, jiya Litinin, ranar farko ce ga ranaku uku da ake zaman makoki don nuna babban alhani ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a wurin Wenchuan na kasar Sin. A wannan rana, bi da bi jami'an kungiyoyin duniya daban daban da jakadun kasashe daban daban a Geneva sun je zauren kungiyar wakilan kasar Sin da ke a Geneva don nuna babban alhini ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa a Sin.

A wannan rana da maraice, Mr Sergei Ordzhonikidze, mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya kuma shugaban ofishin majalisar a Geneva ya isa dakin ta'aziyya da aka shirya a zauren kungiyar wakilan kasar Sin. Inda tare da bakin ciki ya shafe mitoci sama da 10 yana rubuta dogon bayanin ta'aziyya a kan littafin ta'aziyya. Bayan haka kuma ya yi hira da Mr Li Baodong, jakadan kungiyar wakilan kasar Sin a Geneva don nuna alhini da jejeto. Ya ce, "mummunar girgizar kasar da ta auku a kasar Sin a wannan gami mummunan al'amari ne na bata rai, ta haddasa babbar hasarar rayuka da duniyoyi masu dimbin yawa. Ina fatan jama'ar kasar Sin za su fitar da kansu daga wannan bala'i tun da wuri, kuma za su sami nasara a kan bala'in kamar yadda suka yi a da."

Cibiyar kudu wata kungiyar gwamnati da gwamnati ce da ke kushe da kasashe masu tasowa sama da 30. Yayin da Mr Yash Tankon, shugaban zartaswa na cibiyar ke nuna juyayi da jejeto ga mutanen da bala'in ya shafa, ya kuma bayyana muhimman abubuwa uku da suka shaku cikin zuciyarsa. Ya ce, "abubuwan da suka burge ni suna da yawa. Bayan aukuwar bala'in, kasar Sin ta yi dukan abubuwan da take iya yi, har ta yi amfani da jiragen sama don yaki da bala'i da ceton jama'a, wannan ya shiga cikin zuciya sosai. Sa'an nan imanin da shugabannin kasar Sin da jama'arta suka nuna bayan aukuwar bala'in ya shiga cikin zuciya sosai, ka zalika bayan aukuwar bala'in Sinawan da ke zama a kasashen ketare sun hada kansu gu daya don ba da taimakonsu wajen yaki da bala'in, wannan ma ya shiga cikin zuciya sosai."

A lokacin da wakilin gidan rediyo kasar Sin ke tsayawa a dakin ta'aziyyar cikin awa 1 da wasu mintoci, ya ga jakadun kungiyoyin kasashe misalin goma kamar Somali da Bosnia da Herzegovina da Brazil da Kambodiya da Switzerland da Rasha da Japan da sauransu wadanda suka isa dakin don nuna ta'aziyya.

Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a Sin, ba ma kawai kasar Rasha ta aika da dimbin kayayyakin agaji zuwa kasar Sin ba, hatta ma ta aika da kungiyar ba da agaji zuwa wuraren da bala'in ya galabaita, don shiga aikin gano wadanda ke da rai. Da Mr Valery Loshchinin, jakadan kasar Rasha ya tabo magana a kan wadannan abubuwa, sai ya ce, Rasha da Sin kasashe ne da ke makwabtaka da juna, kuma su aminai ne. Ya kara da cewa, "mu aminai ne masu arziki, kuma za mu ci gaba da yalwata irin wannan dangantakar zumunta. Muna da ra'ayoyin bai daya a kan batutuwa da yawa, kuma huldar siyasa da ke tsakaninmu ta yi ta samun bunkasuwa."

Kasar Japan kasa ce da ke makwabtaka da kasar Sin. Jama'ar kasar Japan sun ba da babban taimako wajen yin ayyyukan agaji a kasar Sin. Da zuciya daya, Mr Ichiro Fujisaki, jakadan kasar Japan ya nuna juyayi da jejeto ga mutanen Sin da bala'in ya galabaita. Ya ce, a madadin gwamnatin kasar Japan da jama'arta, ina nuna babban alhini da juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a kasar Sin a wannan gami."

A ran 19 ga wata, an kira babban taro na karo na 61 na kungiyar kiwon lafiya ta duniya a babban zauren Turai na majalisar dinkin duniya da ke a Geneva. A gun bikin bude taron, Jane Holton, shugabar babban taron ta bukaci dukan mahalartan taron da suka tashi tsaye, suka yi shiru don nuna alhini ga mutanen kasar Myanmar da suka mutu a sakamakon mahauciyar guguwa da mutanen kasar Sin da suka mutu a sakamakon girgizar kasa.

Dukan wakilan kasashe 193 na kungiyar kiwon lafiyar duniya sun tashi tsaye sun yi shiru cikin minti daya don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon bala'in. (Halilu)