Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 14:24:21    
Gamayyar kasa da kasa sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta kasar Sin

cri

A ran 19 ga wata, gamayyar kasa da kasa sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ta hanyoyi daban daban tare da jama'ar kasar Sin.

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya je ofishin zaunaniyar tawagar kasar Sin dake MDD a ran 19 ga wata don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan. A cikin kundin nuna ta'aziyya, ya ce, a gaban hadari mai tsanani, gamayyar kasa da kasa sun nuna goyon baya ga jama'ar masu girma na kasar Sin.

Mataimakin babban sakataren MDD kuma darektan ofishin MDD dake birnin Geneva Sergei Ordzhonikidze ya je ofishin tawagar kasar Sin dake wurin don nuna juyayi ga mutanen da suka mutu a bala'in.

Babban jami'in kungiyar WTO Pascal Lamy shi ma ya je zaunanen ofishin kasar Sin dake wakilci a kungiyar WTO a birnin Geneva don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a ran nan.

A gun bikin bude taron kiwon lafiya na duniya a karo na 61 da aka yi a ran 19 ga wata a birnin Geneva, wakilan kasashe membobi 193 na kungiyar kiwon lafiya dukkansu sun tashi tsaye sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa na kasar Sin da mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in mahaukaciyar guguwa na Myanmar har minti daya.

A ran 19 ga wata, manyan shugabanni da 'yan siyasa na Uganda da Viet Nam da Koriya ta kudu da Bangladesh da Kazakhstan da Faransa da Italia da sauran kasashe sun je ofishoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa da kuma nuna jejeto ga jama'ar Sin dake yin aikin ceto.

Mutane aminan kasar Sin da jakadun kasashe daban daban sun je hukumomin kasar Sin dake wakilci a kasashen waje a ran nan don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa.(Lami)