A kwanakin baya, gamayyar kasa da kasa sun ba da agaji ga yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa na kasar Sin ta hanyoyi daban daban.
An kai kayayyakin agaji ton 16 na mataki na farko da asusun yara na MDD ya bayar zuwa birnin Chengdu ta jiragen sama soja 2 a ran 19 ga wata. Wani jirgin sama dake dauke da asibiti da likitoci da magunguna na Rasha ya tashi daga birnin Moscow a ran 19 ga wata da dare zuwa birnin Chengdu na lardin Sichuan.
Gwamnatocin kasashen duniya sun ba da agaji ga kasar Sin daya bayan daya. Ofishin 'yan gudun hijira na MDD da kungiyar makaurata ta duniya da sauran kungiyoyin duniya su ma sun ba da kudin agaji ga kasar Sin.
Shugabannin Nijeriya da Latvia da Bolivia da Armenia da Masar da Croatia da Macedonia da kuma sauran kasashe da shugabannin bankin raya Afrika da kungiyar WTO da kungiyar makaurata ta duniya da kawancen sadarwa na duniya sun nuna juyayi ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban.(Lami)
|