Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 18:05:56    
Kasar Sin ta tsai da ranakun zaman makoki na kasar domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa

cri

Da misalin karfe 4 da minti 58 na ran 19 ga wata da asuba, a babban filin Tiananmen da ke nan birnin Beijing na kasar Sin, a karkashin amon taken mulkin kasa, an tayar da tutar kasa mai launin ja kuma mai taurari 5, wanda kuma ke wakiltar mutuncin kasa, bayan da tutar ta kai kolin sandar, kuma an saukar da ita zuwa rabin sanda. Kasar Sin ta yi haka ne duk domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon babbar girgizar kasa da aka yi a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Da akwai sanyi kadan da sassafe a babban filin tiananmen, amma dubban mutane 'yan birnin sun tsaya cif tare a filin domin nuna girmamawa ga tutar kasa. Bayan bikin tayar da tuta, wakilinmu ya samu labari daga wajen wata yariya da ubanta na birnin Beijing. Sunan ubanta Tian Guanghui, diyar kuwa Tian Sangshan.

Diyar ta ce, "Daga cikin mutanen da suka muta da akwai yara wadanda shekarunsu sun yi daidai da nawa. Da akwai yara da yawa wadanda aka danne su karkashin buraguzen gine-gine, sabo da haka na yi bakin ciki sosai."

Ubanta kuma ya ce, "Ni ma na yi bakin ciki kwarai, amma ina jin cewa a gaban wannan bala'in girgizar kasa, mutanen kasar Sin suna hadin gwiwa fiye da kowane lokaci na da."

Mr. Joe Bircher, dilibin Amurka da ke karatu a kasar Sin shi ma ya halarci bikin tayar da tutar kasa da aka yi yau a filin Tiananmen, ya ce, "Ina jin tausayi kwarai sabo da mutane da yawa sun mutu, ba dama mu hana aukuwar girgizar kasa. Amma kasar Sin ta yi aiki da kyau sosai, ta yi matukar kokari, lalle tana da kyau sosai." (Umaru)


1 2