A ran 19 ga wata da safe, bi da bi ne, jakadun kasashen waje 80 da ke kasar Sin, da wakilan kungiyoyin duniya suka je ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon babbar girgizar kasa da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.
Jakadan kasar Japan da ke kasar Sin Mr. Yuji Miyamoto ya gaya wa manemiyar labari na Gidan rediyon kasar Sin cewa, kungiyar ba da agaji ta girgizar kasa ta kasar Japan za ta yi kokarin da take iyawa wajen neman wadanda ke da sauran numfashi. Gwamnatin kasar Japan za ta hada kanta da gwamnatin kasar Sin a yunkurin sake gina kasa. Mr. Yuji Miyamoto yana fatan kasashen Japan da Sin za su kara hada kansu wajen yaki da girgizar kasa. Jakadun kasashen Amurka da Rasha da Spain da kuma Canada dukkansu sun bayyana cewa, kasashen hudu za su kara ba da taimako ga kasar Sin. Jakadun kasar Afirka ta kudu da Korea ta kudu da dai sauransu sun fadi cewa, ko da yake jama'ar kasar Sin sun gamu da babbar girgizar kasa, amma sun yi imani cewa, za su shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara.(Danladi)
|