Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 15:11:49    
Bangaren soja na kasar Sin ya yi iyakacin kokarin aiwatar da aikin ceton bala'in girgizar kasar Sin

cri

A gun taron da ofishin bayar da labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya a ranar 18 ga wannan wata, kakakin ma'aikatar tsaron kasa ta kasar Sin babbar kanar Hu Changming ya bayyana cikakken aikin da bangaren soja ya yi. Ya bayyana cewa, muna mayar da aikin ceton rayuka da dukiyoyi na jama'a bisa matsayin ma'aunin koli na aikinmu, in da akwai 'yar fata, to za mu yi kokari da ninki 100. Alal misali, wata rundunar sojoji 'yan sanda ta aikin ko ta kwana da ke kunshe da mutane 200 sun fid da tsoron ruwan sama sun yi tafiya cikin mawuyacin hali sosai a kan hanyar tsaunuka da tsawonta ya kai kilomita fiye da 90 cikin sa'o'i 21, a karshe dai sun shiga babban garin gundumar Wenchuan. Wata rundunar 'yan ko ta kwana na sojojin sama na kasar Sin sun sauka wuraren da suke fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai ba tare da samun takardun yanayin sararin samaniya da aka samar musu da kuma jagoranci da aka yi musu ba. Sojoji da hafshoshi na wata rundunar soja suna ta aiki wurjanjan cikin sa'o'i 40, bayan sauyawar da suka yi har sau da yawa kan tsarin ba da ceto ga bala'in ba tare da kasala ba, a karshe dai sun ceci wata yarinya da ke da shekaru 11 da haihuwa. Kai, irin wannan lamarin yana aukuwa a kowace rana a wuraren da bala'in ya shafa.

Mr Hu Changming ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 18 ga wannan wata da karfe 4 na yamma, yawan sojoji da sojoji 'yan sanda da suka tafi wuraren da bala'in ya shafa don ba da ceto ya wuce dubu 110. bangaren soja na kasar Sin zai ci gaba da tura jiragen sama fiye da dubu da kuma yin amfani da na'urori da yawansu ya kai dubu 110 don shiga aikin ba da ceto, sa'anan kuma bangaren soja ya aika masu aikin jiyya da likitoci da yawa don zuwa wuraren da bala'in ya shafa don ba da ceto, haka kuma yana jigilar magunguna da kayayyaki da yawa zuwa wuraren .

Bangaren soja ma ya kafa tsarin ba da hadadden jagoranci na matakai daban daban, sa'anan kuma ya kuma yi amfani da tauraron dan adam da manyan injuna don ba da ceto ta hanyar kimiyya. babbar kanar ta rundunar soja Ma Gaihe ya bayyana cewa, a duk lokacin da muka yi aikin ceto, tun daga farko har zuwa karshe, muna ba da ceto ta hanyar kimiyya tare da yin amfani da sauran kayayyakin da ke da amfani a fannoni da yawa.

Yanzu, kodayake lokaci ya riga ya wuce sa'o'i 72 da aukuwar lamarin girgizar kasa , amma sojoji da sojoji 'yan sanda suna nan suna ci gaba da aikin ba da ceto. (Halima)


1 2