---- Kwanan baya, Mr. Huo Wei, shugaban ofishin binciken ilmin Tibet na jami'ar Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin ya bayyana cewa, sai nasarorin da aka samu wajen bincike da kuma kiyaye kayayyakin tarihi na Tibet kawai ma sun iya yin watsi da ra'ayi na wai "gushewar al'adu".
Tun daga farkon karnin da ya wuce, mutane masu binciken kayayyakin tarihi da masana ilmin Tibet na jami'ar Sichuan suka fara aikin bincike da kuma kiyaye kayayyakin tarihi na Tibet. Cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, masana masu binciken kayayyakin tarihi sun yi bincike daga fannoni da yawa.
Mr. Huo ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya takan ware makudan kudade domin ba da kariya da yin gyare-gyare ga kayayyakin tarihi da na addinin jihar tibet, sa'an nan kuma an kiyaye da kuma nuna kayayyakin tarihi da yawa a jihar Tibet ta hanyar kafa dokokin kayayyakin tarihi da kyautata kasuwanni.
---- Kwanan baya a titunan birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin, ana iya ganin jajayen takardu da aka manna a kofofi da tagogi na bayan wasu motoci, wadanda a jikinsu aka rubuta kalmomi kamar haka, "Nuna goyon baya ga wasannin Olimpic, Beijing zai kara kokari". Jama'ar jihar Tibet suna nan suna bayyyana ra'ayinsu na kishin kasa ta hanyoyi daban-daban.
Mr. Guo Qingshan, jimi'in wani kantin birnin Lhasa ya bayyana cewa, kwanan baya shi da masana'antu 2 daban na birnin Lhasa sun shirya bikin "Yin wasannin Olimpic tare, da nuna kauna ga kasar Sin", suna fatan za a manna irin wadannan jajayen takardu a kan dukkan motocin birnin.
Kuma ana nan ana yin bukukuwan kishin kasa a cikin jimi'o'in jihar Tibet, kwanan baya samari masu hidima na sa kai na jami'ar jihar Tibet, an fara yin bikin "Yin hidima ga wasannin Olimpic ta hanyar yin murmushi", da akwai samari fiye da 300 da suka zo daga kabilu daban-daban sun sa hannu nan da nan a wurin domin shiga jerin masu hidima na sa kai, sun bayyana cewa, za su ba da taimakonsu domin mika wutar wasannin Olimpic a jihar Tibet da kolin tudun Jomo Langma.
Mr. Kelzang Yeshe, shahararen masanin ilmin Tibet, kuma mai bincike na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'umma ta jihar Tibet ya bayyana cewa, tun tuni wasu kasashen yamma sun yi bakin nufin sa hannu kan matsalar Tibet, amma mummunan tashin hankalin da aka yi a ran 14 ga Maris ya sake tone mugun nufinsu. Ya bayyana cewa, a halin yanzu, bisa matsayinsa na wani mutumin jihar Tibet, aikin da zai yi domin kishin kasa shi ne ya tsaya haikan domin kiyaye dinkuwar kasa daya da dorewar zaman al'umma, da tafiyar da aikinsa da kyau.(Umaru)
|