Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 15:00:13    
An sami sabon ci gaba wajen raya kasuwannin wasannin Olympic na Beijing don moriyar juna

cri

Yayin da ranar da za a fara yin wasannin Olympic na Beijing ke kara kusantowa, an shiga lokaci mai muhimmanci don raya kasuwannin wasannin Olympic. Yanzu, an riga an kammala aikin samun masana'antun da za su taimakawa wasannin Olympic na Beijing. Kyawawan masana'antun gida da waje da yawa sun zama 'yan kasuwa da za su taimaka wa wasannin Olympic na Beijing. Ba ma kawai wadannan masana'antu za su taimakawa wasannin Olympic a fannin kudi da kayayyaki da fasaha da hidima ba, har ma za su nuna himma wajen aiwatar da harkoki domin jin dadin jama'a.

Da Madam Yuan Bin, minista mai kula da harkokin raya kasuwanni ta kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ta tabo magana a kan wannan, sai ta ce, "wadannan masana'antu suna bayar da bayanai a kan kayayyakinsu da samfurorinsu da gasar wasannin Olympic da wasannin Olympic na Beijing gu daya, yin haka ba ma kawai suna kara daga matsayinsu ba, har ma sun yi bayani a kan ilmin wasannin Olympic da burin wasannin Olympic da manufarsa, haka kuma sun yi bayani a kan wasannin Olympic na Beijing, don haka kamata ya yi, a ce, suna ba da babban taimako ga wasannin Olympic."

Wasannin Olympic na Beijing ya sami taimako daga wajen dimbin manyan masana'antun kasa da kasa. Wadannan manyan masana'antu suna amfani da damar da suka samu daga wajen wasannin Olympic don yin talla ta hanyoyi daban daban, suna ba da taimakonsu ga zamantakewar al'ummar kasar Sin.

Malam Park Yoon Heyi, babban direktan reshen Kamfanin Sumsong a babban yankin kasar Sin wanda ya ba da hadin kai ga hukumar wasannin Olympic ta duniya da aikin mika wutar wasannin Olympic ya bayyana cewa, "mun zabi fararen hula masu girma 265 ta hanyar jefa kuri'a a kan Internet, dukanninsu sun yi zafin nama ga aikin raya kasa da zamantakewar al'umma. Ko da yake ba su yi suna sosai ba, amma su ba da taimakonsu ga aikin raya zamantakewar al'umma da al'adu a kasar Sin ba tare da son kai ba. Dukanninmu muna farin ciki da su da kuma sa musu ran alheri. Sabo da haka a ganin kamfanin Sumsong, sun cancanci wakiltar jama'ar kasar Sin wajen shiga harkokin mika wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing. "

"Shirya wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba" wannan alkawari ne da aka dauka wajen shirya wasannin Olympic na Beijing, kuma manufa ce da masana'antu masu taimaka wa wasannin Olympic na Beijing ke son cim mawa. Malam Peng Deming, shugaban kwamitin gudanarwa kuma babban jami'in zartaswa na babban kamfanin General Electric wato GE a kasar Sin ya bayyana cewa, kamfaninsa zai yi iyakacin kokari wajen tsimin makamashi ta hanyar kyakkyawar fasaha, don ba da taimako ga kasar Sin wajen samun ci gaba mai dorewa da shirya wasannin Olympic na Beijing ba tare da gurbata muhalli ba. Ya kara da cewa, "Kamfanin GE ya dauki alkawari a tsanake cewa, muna farin ciki da samar da karfinmu da fasaharmu da kuma kudinmu wajen taimakon birnin Beijing da ya tabbatar da shirya wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba. Mun yi ayyuka masu yawa wajen yin ma'amala tare da bangarori daban daban don nuna kyakkyawan sakamakon da aka samu wajen gudanar da shirin yin wasannin Olympic na Beijing. Mun yi imani cewa, za mu nuna wa kasashen waje wani bangaren birnin Beijing da ake takama da shi."(Halilu)