
Ran 18 ga wata, bayan an sake nazarin kundin girgizar kasa fila fila, hukumar kula da girgizar kasa ta kasar Sin ta gyara karfin girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan daga digiri 7.8 zuwa digiri 8.0 na ma'aunin Richter. Masu ilmin hukumar sun bayyana cewa, gyara karfin girgizar kasa ya dace da ka'idar da kasashen duniya suka saba bi.

A ran 12 ga wata, bayan bala'in girgizar kasa ya faru a lardin Sichuan, da sauri ne cibiyar sa ido kan girgizar kasa ta kasar Sin ta sanar da karfin girgizar kasa na digiri 7.8 bisa bayanan da aka samu. Bayan haka, bisa ka'idar da kasashen duniya suka saba bi, an sake nazarin kundin girgirzar kasa fila fila ciki har da bayanan da cibiyoyin sa ido kan girgizar kasa na kasa da kasa suka samu, an tsai da karfin girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan na digiri 8.0 na ma'aunin Richter.
|