Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 12:20:46    
Tabbas ne gwamnatin kasar Sin za ta ba da taimako ga mutanen da ke shan wahalar bala'i a cewar Hu Jintao

cri

Ran 18 ga wata, a lokacin da Mr. Hu Jintao shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin sojoji na tsakiya na kasar Sin ya yi rangadin ayyukan ceto da yaki da bala'in girgizar kasa a garin Shifang na lardin Sichuan, ya ce, tabbas ne gwamnatin kasar Sin za ta ba da taimako ga mutanen da ke shan wahalar bala'in don cin ma nasarar yaki da girgizar kasa.

Shugaba Hu Jintao ya je wani wurin da ke kwanta da mutanen da ke shan wahala da ke garin Shifang domin nunawa musu jejeto. Ya yi magana ga sojojin da ke yin ayyukan ceto, ya ce, muna cikin halin gaggawa, dole ne mutane masu yin ayyukan ceto su yi kokari ba tare da tsayawa ba domin ci gaba da neman wadanda ke da sauran numfashi.

Ban da haka kuma, shugaba Hu Jintao ya bukaci a kara kwanta da hankulan mutane da ke shan wahala, ta haka domin karfafa limaninsu, da kuma kawar da matsaloli, da kuma tayar da gidaje.

Ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 2 na yamma, an riga an samun mutane 32,476 da suka mutu, sauran mutane fiye da dubu 220 a lardunan Sichuan, da Gansu, da Shaanxi sun jikkata a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya faru a ran 12 ga wannan wata.