Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 17:55:43    
Waiwaye adon tafiya(3)----sun sadaukar da kyawawan shekarunsu ga sashen Hausa na CRI

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wato shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Halima da Sani da Halilu da Umaru, sun kasance wasu daga cikin tsoffin ma'aikatan sashen Hausa, kuma sun shafe shekara da shekaru suna kasancewa tare da masu sauraronmu. Su Halima da Sani da Halilu da dai sauransu, sun fara aiki a sashen Hausa ne a kimanin shekarar 1964 zuwa 1970, kuma ma iya cewa, sun sadaukar da kyawawan shekarunsu kimanin 40 ga sashen Hausa na rediyon kasar Sin, kuma sun gane ma idonsu yadda sashen Hausa yake ta bunkasa, yadda yaro ya girma ya zama dattijo. To, yanzu bari mu saurari labaransu.

A lokacin da aka kafa sashen Hausa, Sinawa kusan ba wanda ya iya Hausa, kuma Sinawa ma'aikatan sashen Hausa sun koyi harshen Hausa ne daga wani malami mai suna Amada Bacha da aka gayyace shi daga kasar Nijer. To, amma daga baya, an fara koyar da harshen Hausa a jami'o'i biyu da ke nan birnin Beijing, wato jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing da Jami'ar koyar da ilmin watsa labarai ta Beijing, kuma Halima da Umaru da Sani da Halilu dukansu sun koyi harshen Hausa ne cikin jami'o'in biyu. Malama Halima ta ce, ta koyi harshen Hausa ne domin amsa kirar da marigayi Zhou Enlai, tsohon firaministan kasar Sin, ya yi, na nuna goyon baya ga kasashen Afirka. Ta ce, "Na fara koyon harshen Hausa a jami'ar koyar da ilmin yada labarai ta Beijing, a wancan lokaci, wani malami mai suna Hamidu ya koya mana, shi dan asalin Nijer ne. A wancan lokaci, mu ba mu san harshen Hausa ba ko kadan, amma fa a wancan lokaci, tsohon firaministan kasar Sin, Zhou Enlai, ya mai da hankali sosai ga harkokin Afirka, kuma ya ce, ya kamata kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen Afirka. Amma fa a kasar Sin, babu wanda ya iya Hausa, shi ya sa wasu malamanmu sun zo daga kasar Nijer, sun shiga jami'armu, akwai malamanmu guda biyu, wani ya koya mana, wani ya koya wa aji na gaba."

A lokacin da suke koyon harshen Hausa a jami'a, fahimtarsu game da al'adun Hausa ma sai kara karuwa take yi a fannoni daban daban. Sun ce, a lokacin, burinsu shi ne fadakar da jama'ar Sin a kan Afirka da kuma fadakar da jama'ar Afirka a kan kasar Sin, su karfafa dankon zumunci a tsakaninsu. Bayan da suka gama karatu, sai bi da bi ne suka kama aiki da sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Malama Halima ta tuna da cewa, "Lokacin da na soma aiki a sashen Hausa, lokaci ne da ya yi daidai da lokacin cika shekaru 7 da sashen Hausa ya fara watsa labarai ga kasashen yammacin Afirka. A wancan lokaci, ma'aikatan sashen Hausa ba su da yawa, ma'aikata 7 ne kawai a wancan lokaci, daga cikinsu, da akwai wani ma'aikacin da ya zo daga kasar Nijer, wato malam Hamidu."

Kusan dukan tsoffin ma'aikatan sashen Hausa irinsu Halima da Halilu da Sani da Umaru, sun taba zuwa kasashen Hausa karatu, ko ABU Zaria ko BUK Kano, don inganta ilminsu game da Hausa. Malam Halilu, wanda ya taba karatu a jami'ar ABU, ya ce, "A shekarar 1985, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta aika da ni zuwa Nijeriya, don kara zurfafa ilmina na Hausa a jami'ar A.B.U. ta Zaria, ta jihar Kaduna, sabo da haka, a nan, ina so in isar da dubun gaisuwa ga shugabanni da malamai na jami'ar Ahmadu Bello. Na tuna, a lokacin da nake karatu a sashen koyon harsunan Nijeriya da na Afirka, shugabannin jami'ar sun taimake mu a wajen zaman rayuwarmu, malamanmu kuma, sun yi kokari sosai wajen koya mana harshen Hausa a fannonin adabi da tarihi da nahawu da wakoki da fassara da dai sauransu, bisa koyawarsu, ilmina na Hausa ya karu sosai, sabo da haka, ina yi musu godiya da fatan alheri."

Ban da karuwa da ilmin Hausa, akwai kuma sauran abubuwan da suka burge su. malam Umaru, wanda ya taba karatu a jami'ar Ahmed Bello, ya ce, "Na taba zuwa jami'ar ABU Zaria, don nazari kan harshen Hausa. Na kulla zumunci sosai tare da aminai na Nijeriya. A cikin wani lokaci na bayan wannan, muna ta aikawa juna wasiku, kuma har ila yau, ina rike da hotunan da muka dauka tare, lalle, a wancan lokacin da nake karatu a Nijeriya, sun ba ni zurfaffiyar alama a zuciyata har duk tsawon raina. Sabo da haka, bari in dauki wannan dama, wato ranar cika shekaru 45 da bude sashen Hausa na rediyon kasar Sin, ina isar da kyakkyawar gaisuwata ga dukan aminai da suka taba ba ni taimako da kulawa a lokacin da nake Nijeriya."

Da Halima da Sani da Umaru da Halilu dukansu sun shafe shekaru kimanin 40 suna aiki a sashen Hausa, kuma ma iya cewa sun gane ma idonsu yadda sashen Hausa ya bunkasa, kuma sun kasance tamkar su ne suka ciyar da yaro da ya girma ya zama dattijo. A cewarsu, abin da ya fi burge su shi ne yadda sashen Hausa ya bunkasa cikin sauri tare kuma da samun manyan sauye-sauye. malama Halima ta ce, "A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sashen Hausa ya sami cigaba sosai, tun daga shekarar bara, a kowace rana, yana watsa labarai da bayanan musamman da wake-wake da kide-kide da sauran shirye-shirye har awoyi shida daga rabin awa a da."

Malam Halilu shi ma ya tuna da cewa, "A farkon lokacin da na fara aiki a sashen Hausa, mun yi amfani da keken rubutu wajen shirya labarai da fassara su, kuma mun dauki murya da faifai, yanzu muna aiki ta hanyar zamani, muna amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen shirya labarai da fassara su da kuma daukar murya da sauransu. Idan an kwatanta halin aiki da muke cikin yanzu da na da, ko shakka babu, a ce, sashenmu ya sami babban cigaba.

A lokacin da su tsoffin ma'aikatan sashen Hausa suka waiwayi kyawawan shekarunsu da suka sadaukar ga sashen Hausa, sun ce, "kwalliya ta biya kudin sabulu, kuma hakarmu ta cimma ruwa, aikin da muka yi a sashen Hausa aiki ne mai ma'ana", sabo da ganin yadda suka kara fahimtar juna da tsakanin jama'ar Sin da na Afirka da kuma kara sada zumunta a tsakaninsu. Malama Halima ta ce, ba za ta iya mantawa da yadda masu sauraronmu suka karbe ta da hannu biyu biyu a lokacin da take ziyara a garin Bauchi ba. "A lokacin da na kai ziyara a birnin Bauchi tare da shugaban sashenmu na yanzu, Sanusi, wasu masu sauraronmu sun sami labarin zuwanmu a Bauchi, ba mu yi zaton da cewar, wasu masu sauraronmu sun tare mu a kan hanyarmu zuwa wani wuri ba, sun gayyace mu zuwa shagunansu da gidajensu. Da shigarmu a gidajensu ke da wuya, kai abin mamaki da ya shiga idonmu shi ne, hotona da na sauran ma'aikatan sashen Hausa suna jikin bangon shagunansu, sun yi hira da mu cikin farin ciki sosai, sun dauki hotuna tare da mu, sun ba mu shawarwari da yawa dangane da shirye-shiryenmu, har ma sun ba mu kyaututtukan da suka shirya mana musamman."

Yanzu da Halima da Sani da Halilu da Umaru da dai sauransu dukansu sun yi ritaya daga nan sashen Hausa, sun yi kokarin aiki, kuma sun yi girbi mai kyau. A wannan shekara, sashen Hausa zai dauki sabbin ma'aikatan da suka gama karatu a jami'a, kuma a ganin malam Sani, matasa manyan gobe, sashen Hausa zai samu makoma mai kyau. "Da zuciya daya ne nake fatan sabon jinin sashen, za su kara kokari wajen aiki, su yi koyi da tsoffin ma'aikatan sashen da kuma gwanaye baki, ta yadda za su sami kwarewa wajen aiki. Hausawa su kan fadi cewa, 'kifin rijiya, rijiya ita ce duniyarsa', 'karamin sani kukumi ne', kuma su kan ce, 'rashin sani ya fi dare duhu' . Ko Shakka babu, sashen Hausa zai kara bunkasa yayin da yake samun karin ma'aikata a wannan shekara. Babu tantama, aminai 'yan Afirka za su rinka yin cudanya tare da mu ta kowane fanni, ta yadda za a kara inganta kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka."

Ma iya cewa, tsoffin ma'aikatan sashen Hausa sun sadaukar da kyawawan shekarunsu ga sashen Hausa da masu sauraronsa, sun hau da wata gadar fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da Afirka, muna kuma yi musu fatan alheri. (Lubabatu)