Ran 16 ga wata da safe, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing a birnin Nanchang da ke kudancin kasar Sin. Kafin 'dan wasa Peng Bo wanda ya taba cin zakarar wasannin Olympics ya fara mika wutar yola ta farko, dukkan mutanen da ke wurin sun yi shiru na tsawon minti guda domin nuna jimami ga mutanen da suka mutu a sakamkon bala'in girgizar kasa da ya faru a lardin Sichuan.
Yayin da ake mikawa wutar yola, ana iya ganin tutoci ko ina, an rubuta cewa, "yada ainihin wasannin Olympics, goyon bayan ayyukan fama da bala'in girgizar kasa", da "mika hasken zuci da soyyaya, bari mu yaki da bala'i tare".
Bayan an kammala aikin mika wutar yola, an yi wani babban bikin karbar taimakon kudi domin nuna goyon baya ga ayyuka fama da bala'in girgizar kasa da tayar da gidaje.
|