
Ran 16 ga wata, Mr. Zhang Gu direkatan hukumar harkokin yawon shakatawa ta lardin Sichuan na kasar Sin ya gana da wakilinmu, inda ya bayyana cewa, ya zuwa ran 15 ga wata da karfe 9 na dare, an riga an tabbatar da mutane masu yawon shakatawa 44 sun mutu a cikin bala'in girgizar kasa da ta faru a gudumar Wenchuan, yanzu ana daidaita harkokinsu.
Mr. Zhang Gu ya fayyace cewa, bisa kididdigar da aka yi, yayin da bala'in girgizar kasa ya faru, akwai mutane masu yawon shakatawa 5167 suna wurin. Ya zuwa ran 15 ga wata da karfe 9 na dare, an riga an tabbatar da cewa mutane fiye da 3700 lafiyarwa. Kuma yanzu an riga an ba da agaji mai kyau ga mutane masu yawon shakatawa da suka jikkata. Kuma ana daidaita harkokin mutane masu yawon shakatawa 44 da suka mutu a cikin bala'in.
|