Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 16:33:41    
Sabunta: Kasashen duniya sun ci gaba da bai wa kasar Sin taimako domin gudanar da ayyukan ceto

cri

Bayan da aka yi mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, a kwanan baya, kasashen duniya sun bai wa wuraren kasar Sin da ke shan wahalar girgizar kasar kudaden taimakon da kayayyakin tallafawa daya bayan daya domin nuna wa gwamnatin Sin da jama'ar Sin goyon baya wajen fama da girgizar kasar da gudanar da ayyukan ceto.

Ran 16 ga wata da misalin karfe 9 da minti 45 da safe, ma'aikatan aikin ceto 31 na kasar Japan a rukuni na farko sun isa garin Guanzhuang na gundunar Qingchuan ta birnin Guangyuan, wanda ke daya daga cikin wuraren da ke fi shan wahalar girgizar kasar a wanann karo. Wannan ita ce kungiyar aikin ceto ta farko da kasashen waje suka tura zuwa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasar a Sichuan domin gudanar da ayyukan ceto.

Sa'an nan kuma, a ran 16 ga wata da misalin karfe 6 da yamma, ma'aikatan aikin ceto 50 na kasar Rasha a rukuni na farko sun sauka birnin Chengdu, babban birnin Sichuan. Takwarorinsu na rukuni na biyu kuwa suna kan hanyar zuwa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasar daga Rasha a ran 16 ga wata.(Tasallah)