
Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na lardin Sichuan na kasar Sin a ran 15 ga wata, an ce, ya zuwa ran 15 ga wata da misalin 4 da yamma, mutane kusan dubu 20 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa a lardin Sichuan, an kiyasta cewa, yawan mutanen wadanda suka rasu a girgizar kasa zai wuce dubu 50.

Yanzu mutane masu ceto sun riga sun ceci mutanen da suka jikkata fiye da dubu 60 daga yankunan da ke fama da girgizar kasa, kuma dukkan mutanen da suka jikkata sun riga sun samu jiyya cikin lokaci.
Ran 15 ga wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa gundumar Qingchuan da ke arewacin lardin Sichuan, wadda ta ke fi shan wahalar girgizar kasar. Ya yi wa wadanda ke shan wahalar girgizar kasar bayani da cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin Sin ba su manta da yankunan karkara da ke shan wahalar girgizar kasar ba. Za su tabbatar da ba da isasshen abinci da ruwan sha da tantuna da magunguna, sa'an nan kuma, gwamnatin Sin za ta bayar da kudin alawas wajen sake gina gidaje. (Tasallah)
|