Bayan da aka samu girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin a ran 12 ga wata, ba tare da bata kowane lokaci ba, kasar Sin ta soma aiwatar da ayyukan ceto da ba da agaji cikin saurin da ba a taba gani a da ba. Matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka kuma take aiwatarwa wajen fama da wannan girgizar kasa sun samu goyon baya daga jama'ar kasar, kuma sun sa kaimi da kwantar da hankulan jama'a. A waje daya kuma, sauran kasashen duniya sun yaba wa matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka.
Da farko dai, ayyukan ceto da ba da agaji a yankunan fama da bala'in girgizar kasa suna bayyana yadda kasar Sin take daidaita irin wannan bala'i daga indallahi cikin sauri. Bayan aukuwar bala'in, nan da nan ne, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ba da umurnin soma aikin ceto da ba da agaji. Bayan awa daya da rabi, firayin minista Wen Jiabao ya tashi daga birnin Beijing zuwa yankunan fama da bala'in. A waje daya kuma, dukkan hukumomin da suke da nauyin fama da bala'i daga indallahi bisa wuyansu sun soma aiwatar da shirye-shiryen fama da bala'in cikin sauri. Game da wannan sauri, Mr. Salvano Briceno, direktan ofishin sakatariyar fama da bala'i daga indallahi bisa manyan tsare-tsare ta majalisar dinkin duniya ya ce, "Ana mamaki sosai kan saurin da gwamnatin kasar Sin take ciki wajen fama da bala'in. A cikin shirye-shiryen talibijin, na ga bullowar masu ba da agaji a yankunan da ke fama da bala'in bayan aukuwar bala'in sa'o'i hudu kawai. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai daidai wajen fama da bala'in. Wannan ya ba ni alama sosai, a hakika dai tana da sauri sosai."
A waje daya kuma, kasar Sin tana bayyana karfinta na daidaita harkokin fama da bala'in girgizar kasa. Bayan aukuwar girgizar kasa, hukumomin gwamnatin kasar Sin da rundunar sojan kasar Sin da rundunar 'yan sanda mai dauke da makamai sun hada kan juna cikin sauri domin aiwatar da matakan fama da bala'in. Sabo da haka, an iya isar da masu ba da agaji da kayayyakin jin kai a yankunan fama da bala'in cikin sauri. Mr. Wyndham James, wakilin farko da ke kula da shirin asusun tallafawa yara a nan kasar Sin ya ce, "A cikin irin wannan halin da ake ciki, babu gwamnatoci da yawa a duniya da za su iya tattara kayayyaki da mai da hankulan mutane cikin sauri kan bala'in kamar gwamnatin kasar Sin take yi yanzu."
Bugu da kari kuma, kasar Sin tana bayyana yadda take sauke nauyin da ke bisa wuyanta cikin sauri. Ko da yake babu kyawawan yanayi da hanyoyin mota, amma bayan aukuwar bala'in girgizar kasa kamar minti 10 kawai, hukumar sa ido kan girgizar kasa ta kasar Sin ta bayar da labari ga jama'a nan da nan ta hanyoyi daban daban. Sabo da jama'a suna iya samun hakikanan labaru game da bala'in, ba a tashin hankali a nan kasar Sin ba.
Game da karfin da kasar Sin take bayyanawa wajen fama da wannan bala'in girgizar kasa, ana ganin cewa, dalilan da suka sa kasar Sin take iya aiwatar da matakan ba da agaji su ne, cigaban da ta samu a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha. A waje daya kuma, a cikin wadannan shekaru da yawa da suka gabata, kasar Sin ta samu cigaba sosai wajen kyautata dokoki iri iri. A shekarar bara, an soma aiwatar da "Doka ta fama da al'amuran da suka auku ba zato ba tsammani ta kasar Sin". Kuma tun daga ran 1 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki, an soma aiwatar da "Ka'idar sanar wa jama'a labarun gwamnatin kasar Sin". Mr. Peng Zongchao, wani masanin da ke aiki a jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ya ce, "Dalili daya da ya sanya gwamnatin kasar Sin take iya daukar matakan fama da wannan bala'in cikin sauri sosai shi ne, kasar Sin ta yi kokarinta sosai wajen kyautata tsarin fama da al'amuran da suka auku ba zato ba tsammani."
|