Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 16:55:00    
Ana kasancewa da babbar matsala wajen samar da hatsi yadda ya kamata

cri
Tun daga ranar 5 zuwa ranar 16 ga wata a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, ana yin taro a karo na 9 da aka saba yi na majalisar dokoki ta Pan-Afrika da ke karkashin shugabancin kungiyar tarayyar kasashen Afrika, wato AU, inda aka mayar da matsalar samar da hatsi yadda ya kamata a matsayin babban batu na wannan taro. Taron yana ganin cewa, yanzu ana kasancewa da babbar matsala wajen samar da hatsi yadda ya kamata da karuwar farashin hatsi ta duniya ke haddasa.

Wani jami'in kwamitin kula da harkokin tattalin arziki, da sha'anin noma, da yanayin kasa, da kuma muhalli na kauyuka na majalisar dokoki ta Pan-Afrika, ya yi jawabi a gun taron, inda ya yi gargadi cewa, a shekaru biyar da suka wuce, mutanen da suka gamu da matsalar karancin hatsi daga yankin Afrika sun wuce miliyan 30, yankunan tsakiya da na gabashin Afrika sun fi fama da matsalar, yawan mutanen da ke shan wahalar ya kai kusan miliyan 14.

Manazarta sun nuna cewa, bala'u daga indallahi, ciki har da ambaliyar ruwa da fari, sun kawo mummunar matsala ga sha'anin noma, da na kiwon daddobi a yankin Afrika da ke kudancin hamadan Sahara, bayan haka kuma, karuwar farashin hatsi ta duniya da aka kara samu a kwana a tashi ta kara tsanancewar halin da Afrika ke ciki wajen samar da hatsi.

Kara samun bala'u daga indallahi, wannan ce tsohuwar matsalar da sha'anin noma na Afrika ke fuskanta, amma wasu sabbin dalilai a jere da suka bullo tun 'yan shekarun da suka wuce, su ma suna kawo barazana ga yankin Afrika wajen samar da hatsi yadda ya kamata. A 'yan shekarun da suka wuce, wasu kasashen Afrika sun nemi bunkasa masana'antu da ciniki a gefen daya, a sakamakon haka, ba su bayar da isasshen kudi da nuna goyon baya sosai ga sha'anin noma ba, abin ya haddasa kara raguwar yawan hatsi da aka fitar.

Bayan haka kuma, rikicin makamai da aka samu a wasu yankunan da ke Afrika sun ma sun kawo tasiri mai tsanani ga aikin kawo albarkar noma. Ba kawai rikicin ya hana cigaban sha'anin noma ba, har ma ya haifar da 'yan gudun hijira da yawa, a sanadiyar haka, aka kara tsanancewar matsalar hatsi.

Yanzu, hukumomin da abin ya shafa na M.D.D., da bankin duniya, da kuma bankin raya kasa na Afrika, da dai sauransu suna daukar matakai don magance mawuyancin halin da Afrika ke fuskanta wajen samar da hatsi yadda ya kamata. A farkon watan Afril na shekarar da muke ciki, bankin duniya ya taba sanar da cewa, a kasafin kudi na shekarar 2009, zai kara bayar da taimakon rancen kudi ga sha'anin noma na Afrika daga dalar Amurka miliyan 400 zuwa 800.

A waje daya kuma, bayan da bankin raya kasa na Afrika ya shirya taron majalisu a farkon watan Mayu a kasar Tunisiya, ya bayar da sanarwa cewa, bankin zai kara bayar da taimakon rancen kudi da yawansu ya kai biliyan 1, don taimakawa kasashen Afrika wajen magance matsalar karuwar farashin hatsi. Tare da taimakon rancen kudi na dalar Amurka biliyan 3.8 da ya bayar a da, jimlar rancen kudi da bankin raya kasa na Afrika ya bayar, don bayar da taimako ga sha'anin noma na Afrika ta karu zuwa dalar Amurka biliyan 4.8.

A cikin lokacin taron, majalisar dokoki ta Pan-Afrika ta yi kira ga kungiyar tarayyar kasashen Afrika, da kungiyar abinci da aikin gona ta M.D.D., wato FAO, da kuma sauran hukumomi da su dauki hakikanan matakai masu amfani, don taimakawa kasashen Afrika wajen bunkasa sha'anin noma, da neman dabarar warware matsalar.