Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 16:37:24    
Wata yar kasuwa ta Mongoliya ta rubuta takarda ga jami'in gwamnatin kasar Sin

cri

Dedbilig,wata shahararriyar 'yar kasuwa ce wadda ta yi ciniki tsakanin kasar Sin da Mongoliya, ta kuma auri wani saurayi basine, suna zama a birnin Erlianhot na jihar kabilar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewancin kasar Sin, domin daukaka ci gaban mu'amalan ci gaban tattalin arziki da ciniki na tsakanin Sin da Mongoliya, ta rubuta wasika zuwa ga jami'an gwamnatin wuri inda ta kawo shawarwari ga gwamnatin birnin Erlianhot game da bunkasa kasuwanci da ke kan iyakar kasa.

Dedbilig tana da shekaru 36 da haihuwa a wannan shekara. Yayin da ta kai shekara ta 17, ta karo iliminta na game da masana'antu da wutar lantarki a jami'ar koyon ilimin kimiyya da fasaha ta birnin Shanghai dake gabacin kasar Sin ta shirin tura dalibai zuwa kasashen waje da gwamnatin Mongoliya ta gabatar. Bayan shekaru biyu, Dedbilig ta kamu da wahala, ta kaza biyan kudin makaranta. Shi ya sa ta fara aiki bayan aji ta yadda za ta iya ci gaba da karatunta a kasar Sin."Na fara da aiki a wata karama masana'anta a birnin Shanghai da dare. Aikina shi ne harhada injin Switch, kudin da aka ba ni ya dangana yawan injunan da na harhada. Na kan samu kudin Sin Yuan Hamsin a dare daya." Dedbilig ta kammala karatun a jami'ar tare da kudin da ta samu. A shekara ta 1992 yayin da ta gama karatunta na jami'a, kasar Sin ta shiga wani sabon mataki na kawo sauyi da bude kofa ga kasashen waje, Dedbilig ta ji makomar bunkasuwa ta kasar Sin. A wannan lokaci, abokan karatunta na kasar Mongoliya a kasar Sin sun koma gida, ita Dedbilig ta niyyata ta ci gaba da zama a kasar Sin.

Daga baya Dedbilig ta zo birnin Wenzhou na lardin Zhejiang dake gabacin kasar Sin. Da farko ta fara aiki a wata masana'antar kera injunan switch, kowace rana ta samu kudin Sin RMB yaun dubu. Ta yi farin ciki da samu albashi mai tsoka. A sa'i daya kuma ta fahimci wahalar rayuwa. " A wannan lokaci na yi aiki a wani karamin worshop inda iskar da ke ciki cike da ruwa. Yanayi na da sanyi sosai, na zuba gumi da yawa. Na yi aiki na tsawon shekaru biyu cikin wannan hali."

Kan aikin tukuru da ta yi, zaman Dedbilig a kasar Sin ya fara zauna da gindinsa. Dedbilig ta shiga kaunar kasar Sin wadda take da arzukan al'adu da dabi'u da kuma wurare masu kyaun gani da makoma mai haske, ba ta so ta raba kanta da wannan kasa. Yayin da ta tashi daga wurin mahaifinta sa'ad da ta ke da shekaru 17 da haihuwa, ta fara tunawa da wurin mahaifinta. Ta yi dogon tunani, daga baya ta sami wata dabara,wato ta tafi birnin Erlianhot da ke arewancin kasar Sin.

Birnin Erlianhot yana tsakiyar jihar kabilar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, baki mafita ne daga kasar Sin zuwa kasashen Mongoliya da Rasha da kasashen Turai ta hanyar dogo, kuma muhimmin wuri ne na tattara da barbaza kayayyakin shigi da fici na jihar Mongoliya ta gida da kuma kasar Sin baki daya. A ganin Dedbilig ta fi dacewa da zama a wannan birnin da ya hada kasar Sin da ta Mongoliya.ta ce" idan gwamnatinmu ba ta tuwa ni zuwa kasar Sin domin karatu ba,kila na ci gaba da fama da talauci a matsayin makiyayiya a halin yanzu. Ko da ya ke ba na koma gida, na yi zama a birnin Erlianhot wanda ya kusanci kasata, na iya yin mu'amala da 'yanuwanmu da ba da gudumuwa ga kasarmu."

Da farkon farko, Dedbilig ta yi aikin tafinta ga 'yan kasuwa na Sin da Mongoliya saboda ta kware a fannin sinanci. Daga baya ta fara shiga kasuwanci na tsakanin Sin da Mongoliya. Tare da ci gaban da ta samu, Dedbilig ta bude kamfaninta mai kula da harkokin shigi da fici na ma'adinai. A wannan lokaci ta samo masoyinta wani saurayi na kasar Sin, ta aure shi, ta zama sarakuwa ta kasar Sin, kasar Sin ta zama kasarta ta biyu.

Cikin yin amfani da fiffikon da ta ke da shi a birnin Erlianhot da kuma auratayya da ta yi da basine, Dedbilig ta yi kokarin ba da taimakonta ga ci gaban kasashen nan biyu Sin da Mongoliya. Bisa gabatarwa da ta yi, kamfanoni da yawa na kasar Sin sun shiga kasar Mongoliya su tafiyar da harkokin gina hanyoyin mota da gidaje da kuma yin kayayyakin gine gine. Tare da ci gaban mu'amalar tattalin arziki da cinikin da ake yi tsakanin kasar Sin da Mongoliya, Dedbilig ta gano wasu matsalolin da suke addabar ci gaban kasuwannin birnin Erlianhot na kasar Sin. ta ce" a da 'yan kasuwa da yawa na kasarmu Mongoliya sun zo birnin Erlianhot ne domin daukar hajoji iri iri da suka saye a kasar Sin. A shekarar bara da bana, kashi sama da 80 bisa dari daga cikinsu sun tafi cikin kasar Sin domin saye kayayyaki."

Daga nan a cikin harkokinta na yau da kullum, Dedbilig ta tambayi 'yan kasuwa na Mongoliya kan yadda suke kallon yanayin tattalin arziki na birnin Erlianhot, ta kuma tattara shawarwarinsu kan kasuwannin birnin Erlianhot. A watan Afrila na shekara ta 2007, Dedbilig ta rubuta wata wasika zuwa ga wani jami'in da ake kiransa Zhang Guohua na gwamnatin birnin Erlianhot inda ta bayyana dalilin da ya sa birnin Erlianhot ya rasa 'yan kasuwa na Mongoliya,ta kuma kawo wasu shawarwari domin warware wannan matsala.

Ba abun da akan gani a kasar Sin da wata 'yar kasuwa ta ketare ta rubuta wasika da ta bayyana matsalolin da ke akwai a kasuwannin kasar Sin. Me zai faru Dedbilig ba ta da sanin tabbas. Abun mamaki ne da jami'in gwamnatin birnin Zhang Guohua ya samu wasika,ya dora muhimmanci a kai, ya kawo wasikar a gun taron gwamnatin birnin domin tattauna ta. A ganin jami'in Zhang Guohua matsalolin da Dedbilig ta gabatar daidai ne. ya ce"Dedbilig ta dade tana zama a kasar Sin, ta sane da al'amuran birnin Erlianhot, matsalolin da ta bayyana a cikin wasika, wasu mun sani, wasun kuwa ba mu sani ba, a matsayinta 'yar kasuwa ta Mongoliya,ta yi kasuwanci a kasar Sin, ta bayyana matsalolin da 'yan kasuwa na Mongoliya suka kamu wadanda suka shaida ainihin halin da ake ciki."

Kan matsalolin da aka bayyana a cikin wasikar, Zhang Guohua ya ba da umurni inda ya bukaci sassan da abin ya shafa da su kawo dabara da kuma daukar matakai masu amfani ta yadda za su samu amincewar baki 'yan kasuwa. Ban da wannan kuma Zhang Guohua shi ma ya rubuta wasika ta hanyar e-mail inda da zuciya daya ya gayyaci Dedbilig da ta zama 'yar sa ido kan ingancin kayayyakin ciniki na birnin Erlianhot. Zhang Guohua ya ce"Dedbilig 'yar kasuwa ce mai aiki cikin nitsuwa da cika alkawari, tana fatan cinikin dake tsakanin kasashen nan biyu zai kara bunkasa da zumunci zai kara karfi. A ganina ita mutumiya ce mai sada zumunta ta kuma bayyana abubuwa yadda suka kasance a zahiri, tana aiki domin ci gaban ciniki na tsakanin Sin da Mongoliya da kuma zumuncin dake tsakaninsu."

Dedbilig ta yi farin ciki da ganin muhimmancin da aka dora kan shawarwarin da ta kawo. Dedbilig ta ce" Bayan da na aika da wasika, kwamitin dindindin na gwamnatin birnin Erlianhot ya tattauna matsalolin da na gabatar a cikin wasika,aka kuma aika mini wata wasika ta hanyar e-mail, na yi farin ciki sosai da ganin matakan da aka dauka."

Ga shi a halin yanzu,harkokin kamfanin Dedbilig sun habaka har zuwa kasar Rasha. Tana kai da kawowa tsakanin kasar Sin da Mongoliya da kuma Rasha a duk shekara har ma ta rasa damar komawa gida. Tagwayen da ta haifa sun cika shekaru 11 da haihuwa. Da ganin mamarsu ta sha aiki, sun nuna fahimta da goyon bayan ga uwarsu.Ta ce"mamata ta kan makara komawa gida. Da safe da muka tafi makaranta, maman ba ta gidan, da tsakar rana wani sa'i tana gida wani sa'i ba ta gida. A ganina tana ba da taimakonta domin daukaka ci gaban ciniki dake tsakanin kasashen nan biyu da kara karfin zmunci.da na girma, zan ba ta taimako."

Dedbilig ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa tun tana karami ta bar gida, ta dora muhimmanci kan soyayya da kuma kaunar da 'yan iyalinta suka nuna mata. Ga shi a yau mijinta basine yana kaunarta, tagwayensu mata suna fahimtarta da goyon bayanta, kome wahala da ta sha a waje tana jin dadi idan ta tunar da iyalinta. 

Ta ce"wata rana da na ke aiki a filin ma'adinai na Mongoliya, na gaza samun abinci da abin sha saboda mawuyancin hali. Wata rana ina fama da bugun zuciya a tsakar dare,sai in buga waya zuwa gida. 'ya'yanna sun bukace ni da na sa hankali kan lafiyata. Maganganun da suka yi sun kara karfin zuciyata, ina jin dadin maganganunsu."

A yau Dedbilig tana cike da kuzari,tana farin ciki da kasance a matsayin sarakuwa ta kasar Sin, tana bayyana fiffikonta domin ba da taimako ga kasar Mongoliya da kasar Sin.

Jama'a masu sauraro,wannan shi ya kawo karshen shirinmu na zaman rayuwar Sinawa. Mun gode muku saboda kun saurarenmu sai wannan lokaci na mako mai zuwa za mu sake haduwa. (Ali)