Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 16:34:22    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanmu da wr haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin wanda mu kan gabatar da shi a ko wane lahadi domin shere ku.Muna fatan za ku ji dadin shirin. Sai ku kutso akwatin rediyonku ku saurara.

An yi gwajin DNA domin warware wani rikici. Kwanan baya a yankin mulki na musamman na Hongkong an bayar da goro gayyata ga mata da yara su 107 an yi musu gwajin DNA. An yi wannan gwajin DNA ne bayan da wani mutum da aka haife shia asibitin Fan Yuk a ran 30 ga watan nuwanba na shekara ta 1970 ya ce iyaye na zama tare da shi ba nasa ba ne bisa gaskiya. Daga karshen watan Nuwanba zuwa farkon watan Disamba na wannan shekara jarirai 107 aka haifa a wannan asibiti.

Wata sarakuwa ta yi watsi da dusar kankara wajen tafiya domin mika gaisuwa ta sabuwar Shekara. An sami wata mace mai suna Xiao Xuqiu a garin Xinjing na gundumar Wuning ta lardin Jiangxi wadda ta hau dutsen da kankara ta rufe shi na tsawon sa'o'I goma cikin yin biris da tsanannin sanyin da kankara ta kawo duk domin mika gaisuwar sabuwar shekara a gabannin ranar bikin sabuwar shekara. Sarakuwa ba ta yi zama tare da surukarta ba sabo da mijinta yana aiki a birnin Shenzhe mai nisa daga gidan,sabo da haka a gabanin bikin gargajiya tana so ta je gidan mijin domin gai da iyayensu.Amma an yi kankara mai tsanani,duk da hakata ta niyya ta je wurin kafin lokacin, shi ya sa ta sha wahala kwarai da gaske sabo da tafiya cikin kankara.

Wani mutum ya mutu sabo da cin abinci. An sami wani mutum a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin da ya shake har ya mutu sabo da ya cin irin abincin da ake kira Jiaozhi cikin sinanci a ranar farko ta sabuwar shekara ta sinawa. Da ya ke iyalinsa ya kirawo motar agaji, amma kome ya yi makara ya mutu kafin motar ta zo.

An kama wani saurayi mai laifi bayan da ya koma gida. A lokacin bukukuwan yanayin bazara,wato bukukuwa na sabuwar shekara ta gargajiya ta sinawa,mutanen su kan koma gida su hadu da iyalansu. A wannan shekara wani saurayi mai suna Wang da ya gudu ya koma gida domin haduwa da iyalinsa, da saukarsa a gidan ke da wuya, 'yan sanda sun kama shi sabo da ya aikata laifin yi wa wata mace rauni yayin da ya yi gardama da ita.

Wata mata ta fada cikin rigima. An sami wata mata mai zama kadaici dake bukatar wani masoyi ta hanyar buga talla a cikin jaridu. Bayan da aka buga talla a cikin jaridu, matar nan mai suna Fu Chunling mai shekaru hamsin da haihuwa ta sami wani saurayi mai suna Liu Lin mai shekaru 33 da haihuwa, daga baya suka shiga soyayya. Wata rana Liu Lin ya ce yana so ya kafa wani kamfani amma ba shi da isashen kudi ba,ya ce yana so aron kudi daga wajenta. Da ganin haka, matar ta ba shi kudin Sin Yuan dubu dari biyar. Da saurayin ya samu kudi ya bace, matar ta sanar da 'yan sanda, duk da haka 'yan sanda ba su biyan bukatunta ba sabo da ta ranta masa kudin bisa alkawarin da ta dauka yayin da suke zama tare.

An kafa ka'idojin da'a ga malaman koyarwa na makarantun firamare da na sakandare. Hukumar kula da tarbiyya ta lardin Hunan ta bayar da wani tsarin ka'idoji kwanan baya game da da'a na malaman koyarwa a makarantun firamare da na sakandre. A cikin tsarin ka'idojin an tanadi cewa duk malamin da ba ya aikata bisa ka'idojin da'a ba ba a daukaka matsayinsa duk domin daukaka yanayin da'a na makarantun. An kafa wannana tsarin ka'idojin ne domin an samu wasu malaman koyarwa ba su yi abin da ya kamata su yi a makarantu ba.

Jama'a masu sauraro, kun dai saurari wasu labaru masu ban sha'awa daga nan sashen hausa na gidan rediyo na kasar Sin.muna fatan za mu sake haduwa a wannan lokaci na mako mai zuwa. Mun gode muku saboda kun saurarenmu.