Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 16:33:30    
Zaman rayuwar musulmi na birnin Kashi

cri

Jihar Xinjiang wuri ne da 'yan kabilar Uygur ta kasar Sin ke zama tare, birnin Kashi da ke kudancin jihar Xinjiang shi ne wurin da aka fi amun sigar musamman ta musulmi a jihar, yawan 'yan kabilar Uygur da ke wurin ya kai kashi 90 cikin dari, saboda haka, mutane su kan ce, "ba a isa Kashi ba, to ba a isa Xinjiang ba". Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyara a birnin Kashi, don fahimtar halin zaman rayuwa da musulmin wurin ke ciki, a cikin shirinmu na yau kuma, za mu yi muku bayani kan zaman rayuwar musulmi na birnin Kashi.

Birnin Kashi yana kudancin jihar Xinjiang, mutanen da yawansu ya kai kashi 90 cikin dari a birnin su fito ne daga kabilar Uygur. Yawancin 'yan kabilar Uygur suna bin addinin musulunci, saboda haka, a wannan birni mai sigar addini, akwai masallatai kanana da manya da yawansu ya kai kusan dubu 10, masallacin Hetgah kuma ya fi shahara daga cikinsu.

Masallacin Hetgah yana cibiyar birnin Kashi, yana alamantar tsohon birnin Kashi. An soma kafa masallacin daga shekarar 1442, har zuwa yanzu yana da tarihi na shekaru sama da 500, shi ne kuma daya daga cikin manyan masallatai guda 4 na kasar Sin.

A lokacin da wakilinmu ke isa masallacin Hetgah, lokacin yin sallah ya yi, musulmi daga ko ina na birnin Sun taru a masallacin.

'Dan kabilar Uygur Kamil,yana aiki a masallacin Hetgah, ya yi alfahari kan aikinsa. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "A zaman yau da kullum, mutanen da ke yin sallah a nan sun kai dubu daya zuwa dubu biyu, a ranar Jumma'a, yawansu zai kai kusan dubu goma. A lokacin bikin karamar sallah da na babbar sallah kuma, yawansu zai kai a kalla dubu 70. Bayan da aka cika mutane a masallacin, sauran mutane sun taru a tituna da babban fili. Lallai mutane sun yi yawa sosai."

Babban limamin masallacin Hetgah Cuma Mowlanna Haje ya gabatar da cewa, tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, gwamnatin kasar Sin, da karamar hukumar jihar Xinjiang sun bayar da kudi har sau 11, don yin gyare-gyare kan masallacin, an kara muraba'in filin da ke gaban masallacin, da kara wasu gine-gine, ciki har da dakunan wanka, da na koyar da Alkur'ani, da dai sauransu, ta yadda aka samar da sauki ga musulmi wajen aiwatar da ayyukan addini kamar yadda ya kamata.

Birnin Kashi yana bakin iyakar yammacin kasar Sin, ba ya samun bunkasuwa sosai kan tattalin arziki. Saboda haka, bayar da taimako ga mutane marasa karfi, da taimaka wa musulmi, don su kawar da talauci da samun wadatuwa, wannan ya zama muhimmin aiki na farko a gaban jam'iyya da gwamnatin kasar Sin.

Haji Sabir yana da yara biyar, kuma iyalinsa na fama da talauci. A ko wane wata gwamnati ta bayar musu kudin Sin RMB fiye da 500, don tabbatar da zaman rayuwarsu.

Bayan haka kuma, tun daga shekarar 1999, al'ummar da Haji Sabir ke zama ta soma aiwatar da tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta, dukkan iyalan da yawan kudin da suka samu bai kai RMB 130, suna iya samun kudin tallafi da gwamnatin ta bayar bisa tsarin. 

A 'shekaru biyar da suka wuce, an kafa wata cibiyar horar da fasahar dinki a wannan al'umma, ya zuwa yanzu, an riga an horar da mutane sama da dubu, kuma yawancinsu sun samu aikin yi.

'Yar kabilar Uygur Patime da shekarunta na haihuwa ya kai 17, ta gaya wa wakilinmu cewa, ana horar da su ba tare da biyan kudi ba. Ta ce, "Na koyi ilmomi masu amfani da yawa a nan, kuma za su taimake ni wajen samun aikin yi nan gaba. Bayan da na gama karatuna a nan, zan kafa wani kantin dinki."

A birnin Kashi kuma, wakilinmu ya kai ziyara ga wasu 'yan wasannin fasahar Mukam sha biyu. Fasahar wasanni ta Mukam ita ce, wata babbar irin fasahar wasanni na kabilu daban daban masu bin addinin musulunci, wadda mai cikakken tsari da ke hade da kida, waka, da kuma rawa. A shekarar 2005, kungiyar ba da ilmi da kimiyya da fasaha ta M.D.D. ,wato UNESCO ta mayar da "Mukam ta kabilar Uygur ta jihar Xinjiang ta kasar Sin" da ta zama "Wakiliyar al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kakani zuwa kakani ", a sakamakon haka, a matsayinta na garin "Mukam sha biyu", gundumar Shache ta birnin Kashi ta kara yin suna, kullum ana gayyatar 'yan wasanni na wurin da su yi wasanni a gida da waje.

Tun lokacin yarantakarsa, malam Yusup Tohti ya soma koyon fasahar kide-kiden Mukam daga ubansa, yanzu kuma ya zama kwararre daya kawai da ke iya wasan dukkan kide-kide sha biyu na Mukam a gundumar Shache. Ya taba yin wasanni a biranen Suzhou, da Beijing, da kuma kasashen Japan, da Ingila, da kuma Pakistan, da dai sauransu, kuma ya samu karbuwa sosai. Ya ce, "Yanzu an riga an nuna fasahar Mukam a duk duniya, ana iya kallon wasannin Mukam a kasar Ingila, da kasar Jamus, da kasar Japan, da kasar Faransa, da kuma sauran kasashe, fasahar Mukam da ta fi da cikakken tsari tana nan gundumarmu ta Shache."

A gundumar Shache, akwai wani wurin yawon shakatawa da aka kafa don tunawa da babbar mawakiya da makadiya, wato sarauniya Amannishahan. Masu wansannen al'adu na jama'a, da kuma farar hula su kan isa wannan wurin yawon shakatawa a ran Jumma'a da safe da ran Lahadi, a nan kuma suna wasannin Mukam da kuma kece raini daga fasahar. Yanzu, gundumar Shache ta tabbatar da 'yan wasanni 13 don su yada fasahar Mukam, kuma ta zuba kudi na musamman wajen kafa cibiyar yada fasahar.

Kan matakan da gwamnatin ta dauka wajen nuna goyon baya ga gada da yada fasahar Mukam sha biyu, Memet Tursun, 'dan wasannin Mukam ya ce, "Kasarmu ta ba da tabbaci sosai ga yada fasahar Mukam, gaskiya ne muna jin farin ciki kan wannan. Yanzu, mu tsofaffi ne, kuma a wata rana za mu bar wannan duniya, amma na yi imani cewa, za a kara yada fasaharmu ta Mukam har abada.