Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 15:31:20    
An soma yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Jinggangshan ta lardin Jiangxi

cri

Da safiyar yau 15 ga wata din nan ne, da misalin karfe 8 da minti 8, aka fara zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Jinggangshan ta lardin Jiangxi.

A wajen bikin kaddamar da aikin yawo da fitilar, sakataren kwamitin garin Ji'an wanda ke shugabancin Jinggangshan Mr. Zhou Meng ya yi jawabi cewar, zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Jinggangshan, tsohon yankin juyin-juya-hali na kasar Sin, na da ma'ana ta musamman. Wato haduwar wutar juyin-juya-hali ta kasar Sin da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Jinggangshan za ta sake kunna hasken zukatan jama'ar yankin. A halin yanzu, kasar Sin tana namijin kokarin gudanar da ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane ba tare da kasala ba a lardin Sichuan wanda mummunar girgizar kasa ta yi ma barna. Mutanen Ji'an za su dukufa ka'in da na'in wajen gudanar da ayyukan yaki da bala'in, a wani yunkurin bayar da gudummowa ga ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane.

Tsawon hanyar da aka ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a zangon Jinggangshan ya kai kilomita kusan 15, gaba daya ne masu dauke da torcila guda 208 suka halarci bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Murtala)