Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 14:21:59    
Kasar Sin za ta kara karfi wajen sa ido kan kudi da kayayyakin ba da agaji don yaki da bala'in girgizar kasa

cri

Bisa labari da jaridar "People's Daily" ta bayar, an ce, a ran 14 ga wata, wakilin din-din-din na ofishin siyasa na kwamtin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma sakataren kwamitin kula da harkokin da'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Mr. He Guoqiang ya bayyana cewa, za a kara karfi wajen sa ido kan kudi da kayayyakin ba da agaji don yaki da bala'in girgizar kasa, don tabbatar da ganin mutane masu shan wahalar bala'in sun amfana da su tun da wuri, game da wadansu aikace-aikace na cin hanci, ko raba kayayyki da kudi ba tare da izni ba ko tanadar su da kaurar da su ba domin yaki da bala'In girgizar kasa ba, to za a yanke musu tsatsauran hukumci.

Lokacin da Mr. He Guoqiang ya shirya taron kwamitin kula da harkokin da'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, ya bayyana cewa, za a yi wa jami'a jarabawa ta hanyar gudanar da aikin ba da agaji don yaki da bala'in girgizar kasa. Ya kamata a yabawa jami'ai masu gudanar da aikin ba da agaji cikin himma da kwazo kuma suke da nagartaccen hali, amma game da wadansu jami'ai masu yin sakaci kan aiki ko ja da baya lokacin da suka gamu da wahala, za a yanke musu tsatsauran hukumci bisa tsarin jam'iyyar da na siyasa. (Zubairu)