Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 20:37:27    
Ana isar da kayayyakin jin kai a yankunan da ke samun girgizar kasa a lardin Sichuan

cri

A ran 14 ga wata, lokacin da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Zhang Xiaoning wanda ke kula da aikin ba da agaji a ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa karfe 4 na ran 14 ga wata da yamma, an riga an isar da tantuna dubu 8 da mashimfidin gado dubu 50 a yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan.

Mr. Zhang Xiaoning ya bayyana cewa, bisa shirin da aka tsara, kafin karfe 12 na wannan rana da dare, za a isar da sauran tantuna dubu 25 da 650 a birnin Chengdu, kuma za a isar da sauran kayayyakin jin kai a yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa gobe.

An labarta cewa, ya zuwa yanzu, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta riga ta kebe wa yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa tantuna dubu 120 da mashimfidin gado dubu 220 da rigunan maganin sanyi dubu 170. An isar da yawancinsu a yankunan lardin Sichuan, an kuma isar da wasu daga cikinsu a yankunan lardunan Gansu da Shaanxi da suke kuma fama da bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)