Ran 14 ga wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya je wasu wuraren da suka fi shan wahalar girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, inda ya jagoranci aikin yaki da girgizar kasa da kuma ba da agaji kai tsaye. Ya nuna cewa, yanzu mutane kimanin dubu 100 suna gudanar da ayyukan ceto a Sichuan.
Ran 14 ga wata da safe, Mr. Wen ya isa gundumar Beichuan ta lardin domin dudduba halin da ake ciki a wurin bayan girgizar kasar. Gundumar Beichuan tana daya daga cikin wuraren da suka fi shan wahalar girgizar kasar a Sichuan a wannan karo. A wannan rana da yamma, Mr. Wen ya je gundumar Wenchuan, wato cibiyar girgizar kasa a wannan karo cikin jirgin sama mai saukar ungulu kai tsaye.
Ya zuwa ran 14 ga wata da tsakar rana, sojoji fiye da dubu 120 da dari 5 suna aikin ceto a Wenchuan da Beichuan da sauran wuraren da suka fi shan wahalar girgizar kasa.
Bisa kididdigar da aka samu, yanzu zuwa ran 14 ga wata da misalin karfe 2 da yamma, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar kasa ya kai 14866, a ciki yawan mazauan Sichuan da suka rasu ya kai 14463.(Tasallah)
|