Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 19:40:18    
Iyayen da ke samun matsin lamba sosai a rayuwa za su yi illa ga lafiyar yaransu

cri

Bisa labarin da jaridar Guardian ta kasar Birtaniya ta bayar a kwanan nan, an ce, an gudanar da wani bincike ga yara 120 cikin shekaru 3, kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, watakila iyayen da su kan samu matsin lamba ko nuna damuwa ko jin bacin rai a rayuwa za su yi illa ga lafiyar jikin yaransu.

Binciken da aka gudanar da shi a zamanin da ya shaida cewa, kara samun matsin lamba a rayuwa zai yi illa ga lafiyar kansa, amma ba a yi bincike sosai kan yadda matsin lamba da aka samu zai yi illa ga lafiyar sauran mutane ba.

Sabo da haka manazarta sun gudanar da bincike ga yara 120 da shekarunsu ya kai 5 zuwa 10 da haihuwa da kuma iyayensu har shekaru 3, inda suka bukaci iyaye su rubuta halin da yaransu ke ciki wajen lafiyar jiki. Kuma idan yaransu sun kamu da cututtuka, sai iyaye su rubuta yawan zafin jikinsu. Ban da wannan kuma iyaye su rubuta takartun tambayoyi kan lafiyar tunaninsu da kuma matsin lamba da suka samu da kuma rikice-rikicen da ke cikin gida a ko wadannen watanni shida.

Daga baya kuma manazarta sun gano cewa, ana kasancewa da dangantaka a tsakanin damuwa da kuma bacin rai da iyaye suka nuna da yiyuwar kamuwa da cututtuka da samun zazzabi ga yara. Kuma an labarta cewa, binciken zai ba da taimako wajen kara fahimtar illar da matsin lamba iri iri da ke cikin gidaje cikin dogon lokaci ya yi wa karfin garkuwar jikin yaran da ke da lafiyar jiki.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gabatar muku da wani bayani kan cewa, samun maki mai kyau wajen karatu ga yara yana da nasaba da gwaninta da iyayensu ke nunawa wajen cudanya.

Manazarta na kasar Birtaniya sun gano cewa, ko da yake ana kasancewa da bambanci tsakanin mutane a fannonin matakin tsarin al'umma da dukiya da kuma matsayin al'umma, amma idan iyaye sun iya yin cudanya da sauran mutane kamar yadda ya kamata, kullum yaransu su kan fi sauran yara kyau wajen karatu.

Furofesa Sarah Brown da kuma Furofesa Karl Taylor na jami'ar Sheffield ta kasar Birtaniya sun gudanar da bincike ga iyaye da yaransu 3000 wajen makin da suka samu a fannonin karanta da rubutu da kidaya da kuma bayani na baka lokacin da shekarunsu ya kai 5 da haihuwa, daga baya kuma an kwantanta makin tare da dabi'ar cudanya ta iyayensu. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da yaran da iyayensu suka nuna gwaninta wajen cudanya, makin da suka samu wajen karatu ya fi kyau har zuwa kashi 1 zuwa kashi 4 cikin kashi dari idan an kwatanta da abokansu na karatu wadanda ba safai iyayensu su kan yi cudanya da sauran mutane ba.

Furofesa Taylor ya bayyana cewa, sakamakon yana da sha'awa sosai, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da su ma sun yi bincike ga iyaye kan ilmin da suka samu da kuma matakin tsarin al'umma da suke ciki. Kullum ana ganin cewa, irin wadannan abubuwa biyu sun taka muhimmiyar rawa ga karatun yaransu. Amma sakamakon binciken ya shaida cewa, ko da yake ilmin da iyaye suka samu ya sha bamban, amma harkokin cudanya da suka yi sun taka muhimmiyar rawa ga karatun yara.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)