|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-05-14 19:15:57
|
An isar da kayayyakin jin kai da kasar Rasha ta samar wa kasar Sin a lardin Sichuan
cri
A ran 14 ga wata da yamma, an isar da kayayyakin jin kai da gwamnatin kasar Rasha ta samar wa kasar Sin ta jirgin saman musamman domin fama da bala'in girgizar kasa da ya auku a lardin Sichuan na kasar Sin.
An labarta cewa, wadannan kayayyakin da suke kunshe da tantuna da mashimfida sun kai ton 30. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Rasha za ta samar da sauran kayayyakin jin kai ton 100 zuwa ga lardin Sichuan domin fama da bala'in. (Sanusi Chen)
|
|
|