
Ran 14 ga wata da safe, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya isa gudamar Beichuan ta lardin Sichuan, wadda na daya daga cikin wuraren da ke fi shan wahalar mummunar girgizar kasa a wanan karo, ta haka, ya jagoranci aikin fama da girgizar kasa da kuma gudanar ayyukan ceto kai tsaye.

A dab da wani ginin karatu da ke cikin makarantar midil ta Beichuan, wanda ya rushe a sakamakon girgizar kasa, Mr. Wen ya bayyana cewa, yanzu an riga an aika da ma'aikatan yaki da girgizar kasa da ba da agaji kimanin dubu 100. Wadannan ma'aikata suna gudanar da ayyukan ceto a ko wace gunduma da ko wane kauye, suna iyakacin kokari domin kubutad da mutanen da buraguzen gine-gine suka danne su. Kubutad da mutane yana kasancewa a gaba da kome.
Mr. Wen ya kara da cewa, ko da yake karfin girgizar kasa ya iya haddasa motsin duwatsu da toshe koguna, amma ba zai iya karya aniyar mutane ba. Ya ci gaba da cewa, in mutane sun hada kansu, sun taimakawa juna, sun yi gwagwarmaya tare, to, za su iya jure wahalar bala'in.(Tasallah)
|