Jiya Talata da dare misalin karfe 11 da minti 15, kungiyar ceto ta farko ta isa gundumar Wenchuan ta yankin Aba mai ikon aiwatar da harkokinsa na kansa na kabilun Tibet da Qiang da ya fi shan wahalar babbar girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, wannan ya sanar da cewa, an riga an bude wata hanyar ceton rai a wannan wuri.
Firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao wanda yake jagorancin ayyukan ceto kai tsaye ya bukaci rundunoni da sojoji da 'yanda da ke halartar ayyukan ceto da su bi hanyoyi daban daban, domin shiga cikin gundumar Wenchuan da dai sauran wurare da suka fi shan wahalar girgizar kasar.
Ya zuwa karfe 7 na yamma na ranar 13 ga wata, bisa kididdigar ba ta cikakke ba da aka bayar, an ce, yawan jama'ar da suka rasa rayukansu sakamkon girgirzar kasa ya kai dubu 12 da 12, mutane fiye da dubu 9 har yanzu ba a cece su ba, yawan mutanen da suke bacewa ya kai dubu 7 da 841.
Firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya bukaci a yi kokarin da ake iya, da daukan dukkan matakan da ake iya, domin ceton rayuwar jama'a.(Danladi)
|