Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 19:02:51    
MDD ta buga babban take ga ayyukan yaki da girgizar kasa da kuma bada agaji a kasar Sin

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an yi girgizar kasa mafi tsanani a ranar 12 ga wata a lardin Sichuan na kasar Sin. Hakan ya haddasa mutuwar mutane da kuma hasarar kayayyaki masu yawan gaske. Bayan aukuwar bala'in, bisa jagorancin gwamnatin kasar Sin ne, a yanzu haka dai jama'a duk kasa baki daya suke hadin kansu tamkar mutum daya suna sanya kokari matuka wajen bada agaji ba tare da bata lokaci ba. Ofishi daidaita harkokin jin kai na MDD, da kungiyar kiwon lafiya wato WHO ta majalisar da kuma hukumar MDD mai kula da ayyukan rage bala'u bisa muhimman tsare-tsare da dai sauran hukumomi sun buga babban take ga ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da kuma bada agaji da gwamnatin kasar Sin take yi.

Kakakin ofishin daidaita harkokin jin kai na MDD Madam Elisabeth Byrs ta furta cewa, lallai ta ji kanta saboda kasar Sin ta gamu da irin wannan babbar masifa. Tana mai cewa: ' Ko shakka babu gwamnatin kasar Sin na sanya kokari gwargwadon iyawa wajen samar wa jama'a dake fama da bala'in kayayyakin masarufi iri daban-daban. Na hakkake cewa, za a iya kara ceton wadanda suke cikin kangayen gine-gine sakamakon girgizar kasar'.

Bayan aukuwar bala'in, gwamna tin kasar Sin ta mayar da martani da saurin gaske yayin da take tattara hukumomi daban-daban don su shiga harkokin bada agaji. Firaminista Wen Jiabao shi kansa ne ya je wuraren dake fama da bala'in, inda ya gaida jama'ar da bala'in ya rutsa da su da kuma bada umurni ga ayyukan ceto. Mr.Salvano Briceno, daraktan kula da harkokin rage bala'u na MDD ya furta cewa : " Abun ala'aji ne domin gwamnatin kasar Sin ta mayar da martani da saurin gaske kan bala'in. Daga T.V. ne na ga masu yin ceto suka isa wuraren da bala'in ya rutsa da su kasa da sa'o'i hudu kawai bayan aukuwar bala'in.Lallai gwamnatin kasar Sin tana yin aiki da kyau wajen yaki da bala'in .''

Ko da yake jama'ar kasar Sin suna himmantuwa wajen yaki da bala'in, amma duk da haka suna samun tsaiko saboda kasancewar mugun yanayin sama da kuma na hanyoyin mota. Madam Fadela Chaib,kakakin kungiyar WHO ta fadi cewa : " Ina cike da imanin cewa, kasar Sin za ta cimma nasara wajen yaki da bala'in girgizar kasa saboda ita babbar kasa ce dake da fasahohi da kuma kwararru da dama wajen bada agaji".

Aminai 'yan Afrika, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa, kasashe da kungiyoyi da yawa na duniya sun bayyana fatansu na samar da gudummowa ga kasar Sin. Game da wannan dai, gwamnatin kasar Sin ta nuna sahihiyar godiya. Da yake a yanzu haka ba a samu sharadi ba, shi ya sa kasar Sin ba ta soma karbar tallafi daga ketare ba tukuna. Amma wadannan hukumomi na MDD dukkansu suna so su tallafa wa kasar Sin.

Yanzu, akwai dubu dubatar mutane da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in da ya auku a lardin Sichuan. Lallai wannan ya girgiza zukatan mutane kwarai da gaske! To, ko ana iya yin hasashe kan yanayin aukuwar wannan bala'I daga indallahi? Madam Briceno ta furta cewa: " Lallai da kyar a yi hasashe kan yiwuwar aukuwar bala'in girgisar kasa ko da wassu kasashe ciki har da kasar Sin suna da fasahar yin hasashe cikin mintoci kalilan kafin aukuwar bala'in". (Sani Wang)