Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 08:08:11    
Bayani kan kulob na mahayin sukuwa na Hongkong

cri

A tarihin Hongkong, watan Yuli na shekarar 2005 yana da muhimmanci, dalilin da ya sa aka fada haka shi ne domin a wannan lokaci, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya sanar da cewa, Hongkong zai shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 tare da birnin Beijing. Hongkong yana da dogon tarihin sukuwar dawaki har ya kai fiye da shekaru dari daya. Yanzu dai a karo na farko ne zai dauki bakuncinta domin gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic, haka zai daga matsayinsa na birnin wasan motsa jiki a duniya.

A sabili da haka, an gayyaci kulob na mahayin sukuwa na Hongkong da ya samar da wurin gasa da kuma gine-ginen da abin ya shafa. Kulob din nan kuma ya yi kokarin yin aikin share fage sosai da sosai kuma ya riga ya kammala dukkan ayyuka a watan Yuli na shekarar bara lami lafiya, wato ya fi sauri a tarihin gasar wasannin Olympic.

Direktan ofishin kula da harkokin jama'a na kulob din nan madam Deng Huijun ta yi mana bayani cewa, Kulob nasu ya kashe kudin da yawansa ya kai biliyan daya da miliyan dari biyu domin shirya wurin gasa da gine-ginen da abin ya shafa, ya zuwa yanzu, aikinsu ya kusan gamawa, kuma za su kawo karshen dukkan ayyuka kafin karshen watan Mayu na bana. Game da inganci da matsayi na wurin gasa da gine-ginen da suke shiryawa, madam Deng Huijun ta bayyana cewa,  "Mun hakake cewa, wurin gasa da gine-ginen da abin ya shafa za su kai matsayin koli a tarihin gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic. A cikin gasar gwajin da muka shirya a shekarar bara, aikin da muka yi ya gamsar da kasashe masu halartar gasar sosai da sosai."

A wurin gasa, mun tarar da irin wani rairayi na musamman, an hada rairayin teku tare da irin wani zanen auduga na musamman, idan dawaki suna gudu kan rairayin, kafarsu ba za ta ji rauni ba. Sa'an nan kuma, mun shiga dakin dawaki, an sa AC a ciki, fadin kowanen daki ya kai wajen muraba'in mita 13, kuma an shimfida rairayi a kasa, dawaki suna iya wasa a ciki kamar yadda suke so bayan gasa. To, yaya za a jigilar da dawaki daga filin jirgin sama zuwa nan? Madam Deng Huijun ta ce:  "Kowace shekara, kulob dinmu ya kan shirya manyan gasannin duniya sau biyu, kuma a kullum mun shigo da dukkan dawaki daga kasashen waje, shi ya sa ko shakka babu za mu jigilar da su daga jirgin sama zuwa dakin dawaki dake Sha Tin cikin sauri, wato wajen awa daya kawai."

Ban da wannan kuma, a kan fannin binciken maganin dawaki, babban direktan kula da harkokin raya wasan sukuwar dawaki na Hongkong Kim Mak ya yi mana bayani cewa, cibiyar bincike ta Hongkong tana da isashen fasaha kan wannan, za ta bincike maganin da ake hana amfaninsa a cikin jikin dawakin gasa cikin sauri.

Kyakkyawan aikin da kulob na mahayin sukuwa na Hongkong ke yi ya kago sabon ma'auni ga biranen da za su shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic a nan gaba. Madam Deng Huijun ta ce:  "Kulob dinmu yana goyon bayan gwamnatin yankin musamman na Hongkong da kasarmu sosai da sosai, kuma za mu shirya wata gasar sukuwar dawaki mai kyau."

Shugaban kungiyar wasannin motsa jiki kuma kwamitin wasannin Olympic na Hongkong Timothy Fok ya bayyana cewa,  "Abin farin ciki shi ne Hongkong ya sami iznin shirya gasar, ina fatan dukkan mazauna Hongkong za su yi iyakacin kokari domin shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta Beijing cikin nasara."(Jamila Zhou)