Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 08:06:36    
Gasar wasannin Olympic ta zamanin da da tatsuniyoyin gumaka

cri

A halin da ake ciki yanzu, ana mayar da gasar wasannin Olympic a matsayin bikin duniya, 'yan wasa daga kasashe daban daban sun sa lura kan nune-nunen 'yan wasan kasashensu a gun gasar, kuma sun yi ihu domin sakamakon da suka samu, amma a can can da kuma, gasar wasannin Olympic aikin gabatar da hadaya ce da aka shirya musamman domin gunki Zeus, sarkin gumaka.

Asalin gasar wasannin Olympic ta zamanin da ya shafi tatsuniyoyin gumaka da yawa, wanda ya fi yin suna yana da nasaba da gunkin da ake kira Zeus. Mun ji an ce, baban gunki Zeus yana son mika masa kujerar sarkin gumakansa, don duba lafiyar jiki da basirarsa, sai ya yi fada da Zeus a kusa da Olympia, a karshe dai, Zeus ya lashe babansa ya ci nasara, daga baya kuma ya hau kan kujerar sarkin gumaka a maimakon babansa. Don taya murnar babbar nasarar da ya samu, gunki Zeus ya ba da umurni ga gumaka da su shirya masa babban aikin gabatar da hadaya a Olympia inda babansa ya taba jin dadin aikin. A gun aikin, su kan shirya nune-nunen wasanni, wannan shi ne asalin gasar wasannin Olympic. Daga wannan, ana iya gane cewa, gasar wasannin Olympic ta zamanin da ba gasar wasanni ce kawai ba, amma kashi daya ne daga cikin aikin gabatar da hadaya na addini, wannan shi ma ainihin banbanci ne dake tsakanin gasar wasannin Olympic ta da da ta yanzu.

A kasar Greece ta da, tatsuniyoyin gumakan da aka baza kan gasar wasannin motsa jiki sun yi yawan gaske, alal misali, 'gasar wasannin Isthmian' da 'gasar wasannin Pythian' da 'gasar wasannin Nemea'. Ban da wannan kuma, mun ji an ce, an taba shirya gasar wasannin motsa jiki musamman domin tunawa da matar Zeus.

Game da 'gasar wasannin Isthmian', an ce, a karni 6 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, a kasar Greece ta da, wata rana, wani dolphin ya aika da wani yaro wanda ya riga mu gidan gaskiya saboda ya fadi cikin ruwa zuwa gabar teku, daga baya kuma sarkin Corinth ya binne yaron a Isthmian kuma ya shirya masa gasar wasanni, a kai a kai ne aka mayar da gasar wasannin a matsayin gasar wasannin da aka shirya musamman domin gunkin teku Poseidon. Wasannin gasannin sun hada da wasan tukin kwale-kwale da wasan guje-guje da tsalle-tsalle da wasan jifa da wasan sukuwar dawaki da wasan waka da kida da sauransu, wadanda suka ci nasara sun samu wata hular furanni.

Duk da haka, gasar wasannin motsa jikin da aka shirya a Olympia ta fi girma.(Jamila Zhou)