Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 20:21:32    
Mutane fiye da dubu goma sun mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin

cri

A ran 13 ga wata, Wang Zhenyang, shugaban sashen ba da taimakon agaji na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya yi bayani a birnin Beijing, cewa yanzu yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan ya riga ya kai 11921.

Da misalin karfe 2 da minti 28 na ran 12 ga wata da yamma, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Bayan aukuwar wannan girgizar kasa, ba tare da bata lokaci ba ne, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da muhimmin umurni, inda ya nemi da a ceci mutanen da suka jikkata tun da wuri domin tabbatar da lafiyar jama'ar da wannan bala'i ya rutsa da su. Sannan kuma an kafa ofishin ba da umunin fama da bala'in girgizar kasa da ke karkashin jagorancin firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin. Yanzu firayin minista Wen Jiabao yana lardin Sichuan, don jarorancin ayyukan fama da bala'in.

A ran 13 ga wata da safe, Wen Jiabao ya bayyan cewa, wannan girgizar kasa ita ce wani bala'i daga indallahi mafi tsanani, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen tattara mutane da kayayyaki domin tallafa wa yankuna masu fama da bala'in.

Kuma firayim minista Wen Jiabao ya jaddada cewa, tilas ne za a kammala ayyukan shimfida hanyoyin zuwa yankunan da ke cibiyar girgizar kasa kafin ran 13 ga wata da karfe 12 da dare domin gudanar da ayyukan fama da girgizar kasa da ceton mutane daga dukkan fannoni.(Kande Gao)