Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 20:04:21    
Kwararru sun yi kira da a yi hattara da cutar koda

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. Cutar koda wata cuta ce da ke iya haddasa mutuwar dimbin mutane. Kuma sabo da cutar ba ta nuna alamu a bayyane sosai, shi ya sa mutane da yawa su kan kamu da cutar ba ji ba gani. Yanzu halin da kasar Sin ke ciki wajen shawo kan cutar koda yana da tsanani, shi ya sa ya kamata jama'a su kara yin hattara da cutar. To a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wannan batu.

Koda wata muhimmin bangare ne na jikin dan Adam, ba kawai tana kula da aikin fitar da abubuwa masara amfani da kuma masu guba daga jiki ba, har ma tana iya ba da taimako wajen samun daidaito tsakanin bugun jini da kuma muhallin da ke cikin jikin dan Adam, da kuma takawa muhimmiyar rawa ga jini da kuma kasusuwa. Li Xun, shugaban ofishin kula da daddadun cututtuka masu wahalar warkewa na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu a duk duniya, yawan mutanen da ke kamuwa da daddaddiyar cutar koda mai wahalar warkewa yana ta samun karuwa. Kuma ya kara da cewa, "Mun kara gano cewa, cutar koda tana yin illa sosai, kuma tana kawo mana kalubale iri iri. Cutar tana daya daga cikin munanan cututtukan da ke yin illa sosai ga lafiyar jiki ban da cututtukan zuciya da hauhawar jini da sankara da kuma cutar sukari, haka kuma yanzu ta riga ta zama wata matsalar kiwon lafiyar jama'a a duk duniya."

Furofesa Zheng Falei, likita mai kula da cikin jikin dan Adam na asibitin Xiehe na birnin Beijing yana ganin cewa, ko da yake cutar koda ba ta nuna alamu sosai ba, amma idan an mai da hankali a kanta, to za a iya samun wasu gargadin da cutar koda ta yi. Kuma ya bayyana cewa, "Watakila a farkon lokacin kamuwar daddaddiyar cutar koda mai wahalar warkewa, ba a iya samun alamu a bayyane ba har ma babu alamu, amma tare da bunkasuwar cutar, ana iya samun wasu alamu, alal misali, a kan ji gajiya, ba a son cin abinci, ba a yin barci sosai, har ma wasu mutane su kan samu kunburi."

 

Amma furofesa Zheng ya nuna cewa, ba a iya tabbatar da cutar koda bisa wadannan alamu kawai, shi ya sa tsayawa tsayin daka kan yin binciken lafiyar jiki a ko wace shekara yana da matukar muhimmanci. Kullum ana bukatar yin bincike kan fitsari da kuma koda sau daya a ko wace shekara bayan da shekaru ya zarce 40 da haihuwa. Idan an kamu da hauhawar jini da kuma cutar sukari, to ya kamta a yi bincike a kalla sau biyu a ko wace shekara.

Ban da wannan kuma furofesa Zheng ya ambaci wani batun da ba safai a kan mai da hankali a kai ba a cikin zaman yau da kullum, wato sabo da shan aiki, wasu mutane su kan manta da shan ruwa, haka kuma ba safai su kan yi fitsari cikin lokaci ba. Furofesa Zheng yana ganin cewa, wannan zai yi illa sosai ga koda da kuma lafiyar jiki. Kuma ya kara da cewa, "Ya kamata a yi fitsari kamar yadda ya kamata. Kuma kamata ya yi a sha isasshen ruwa domin samun yawan fitsari, a waje daya kuma a yi fitsari cikin lokaci. Idan an yi fitsari kadan, to wannan ya shaida cewa, ba a samu isashen ruwan a cikin jiki ba, ta haka kaurin wasu sinadarin da ke cikin jiki zai karu. Idan an kara shan ruwa da kuma yin yawan fitsari, to za a ba da taimako wajen rage kaurin mummunan sinadarin da ke cikin jiki. Ban da wannan kuma, idan ana son yi fitsari, sai a yi cikin lokaci. Kasa yin fitsari kamar yadda ya kamata zai haddasa dimbin matsaloli, kamar kamuwa da cututtuka da kuma raunana amfanin koda da dai sauransu. Ya kamata mu magance wannan." (Kande Gao)