Ran 13 ga wata, wasu gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya sun ci gaba da aika da talgiram zuwa ga shugaba Hu Jintao na kasar Sin da kuma firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin, ko kuma ba da sanarwa domin nuna wa kasar Sin jaje bisa mummunar girgizar kasa a gundumar Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin.
Kakakin sashen yada labaru na ma'aikatar kula da abubuwan ba zata ta kasar Rasha ya bayyana cewa, Rasha ta yi shirin tura jirgin saman da ke daukar tawagar ayyukan ba da agaji da ma'aikatar ta tura da likitoci da nas-nas da kuma jerin kayayyakin jin kai zuwa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasa a kasar Sin domin gudanar da ayyukan ceto.
Ban da wannan kuma, firayim ministan kasar Thailand da ministan harkokin waje na Thailand da firayim ministan kasar Singapore da shugaban kasar Romania da shugaban kasar Pakistan da shugaban kasar Korea ta Kudu da wasu sauran shugabannin kasashen duniya sun nuna ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasa, goyon bayan ayyukan yaki da girgizar kasa da ba da agaji da gwamnatin Sin da jama'ar Sin suke gudanarwa da. A sa'i daya kuma, ma'aikatan harkokin waje na kasashen Japan da Isra'ila da Argentina da dai sauransu su ma sun nuna wa kasar Sin jaje.(Tasallah)
|