Ran 12 ga wata da yamma, bayan an yi girgizar kasa mai tsanani sosai a gundumar Wenchuan na lardin Sichuan, wurare dabam daban na kasar Sin sun ba da taimako ga wurin da ke fama da bala'i.
Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa, nan da nan gwamnatin birnin Beijing ta ba da taimakon kudi na RMB Yuan miliyan 3 ga lardin Sichuan. Kuma yanzu mutane da kamfannoni na Beijing suna kokarin ba da kudin taimaka da kayayyaki ga lardin Sichuan ta hanyoyi dabam daban. A birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, an riga an kafa kungiyoyin ba da agaji, za su tafe wurin da ke fama da bala'i nan take idan akwai bukata.
Ya zuwa ran 13 ga wata da karfe 2 da yamma, kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta riga ta sami kudade da kayayyki da yawa da wurare dabam daban na kasar Sin suka ba da wurin da ke fama da bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan, darajansu ya kai fiye da RMB Yuan miliyan 65.
|