Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 17:32:20    
Kasashen duniya suna son hada kansu da kasar Sin domin yaki da girgizar kasa da ba da agaji

cri

Bayan da aka samu mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin a ran 12 ga wata, wasu gwamnatoci da shugabannin kasashe da shugabannin kungiyoyin duniya sun nuna wa kasar Sin jaje, sun kuma bayyana fatansu na bai wa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasa na kasar Sin taimako.

A ran nan, Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya buga wa Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin wayar tarho, inda a madadin Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna wa gwamnatin Sin da jama'ar Sin tausayi sosai da kuma jaje cikin sahihanci, ya kuma yi imani da cewa, a karkashin shugabanci mai karfi daga gwamnatin Sin da shugabannin Sin, tabbas ne mutanen da ke shan wahalar girgizar kasa za su jure wahalhalu, za su sake gina gidajensu. Ban da wannan kuma, ya bayyana cewa, Majalisar Dinkin Duniya za ta yi iyakancin kokarinta wajen taimakawa kasar Sin a fannonin gudanar da aikin ceto da sake gina gidaje.

Fukuda Yasuo, firayim ministan kasar Japan ya aika da wasiku zuwa ga shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao daya bayan daya, inda ya nuna tausayi da jaje ga mummunar girgizar kasa a Sichuan, ya kuma bayyana cewa, Japan za ta yi namijin kokari domin bai wa kasar Sin taimako.

Sa'an nan kuma, shugaba Bush na kasar Amurka ya ba da wata sanarwa, inda ya yi juyayin mutuwar mutane a sakamakon girgizar kasa, ya kuma nuna jaje ga iyalan mutanen da suka rasu da kuma wadanda suka ji rauni. Ya kuma kara da cewa, Amurka ta yi shirin bai wa kasar Sin taimako ta hanyoyin da za su yiwu domin jure wahalar girgizar kasa mai ban tausayi.

Shugaba Dmitri Medvechev na kasar Rasha ya aika da talgiram zuwa ga takwaransa na kasar Sin Hu Jintao domin nuna jaje ga aukuwar mummunar girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin, inda aka yi hasarar rayukan mutane da dimbin dukiyoyi, kuma mutane da yawa suka jikkata. Ya kuma kara da cewa, a cikin halin da ya wajaba, Rasha za ta ba da taimako ga wuraren da ke shan wahalar girgizar kasa a kasar Sin.

Ban da wannan kuma, kwamitin kungiyar tarayyar Turai wato EU ya ba da wata sanarwar cewa, hukumar ba da agajin jin kai ta kungiyar EU tana sa ido kan halin da ake ciki a wuraren da ke shan wahalar girgizar kasa. Louis Michel, mamban kwamitin kungiyar EU mai kula da harkokin bunkasuwa da agajin jin kai ya ce, kwamitin kungiyar EU a shirye yake wajen ba da taimako.

Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya ya nuna ta'aziyya ga wadanda suka rasu a sakamakon girgirzar kasa. Ya kuma jaddada cewa, kwamitin wasannin Olympic na duniya yana son hada kansa da jama'ar kasar Sin sosai domin jure wahalar bala'i.

Kazalika kuma, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Mexico da ta kasar Iran su ma sun nuna wa gwamnatin Sin da jama'ar Sin jaje cikin sahihanci.

Ban da wannan kuma, shugaban kasar Faransa da shugaban kasar Pakistan da firayim ministan Pakistan da shugabar gwamnatin kasar Jamus da firayim ministan kasar Slovenia da shugaban kasar Poland da shugaban kasar Serbia da sarkin kasar Kuwait sun aika da wasika ko kuma talgiram zuwa ga shugaba Hu Jintao na kasar Sin, inda suka nuna jaje ga kasar Sin, wadda take shan wahalar girgirzar kasa mai tsanani. Shugabannin da yawa sun bayyana fatansu na bai wa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasa na kasar Sin taimako. Ban da wannan kuma, kasashen Faransa da Isra'ila da Turkey da Singapore da Kuwait da Colombia da Argentina sun mai da hankulansu da kuma nuna jaje ga kasar Sin bi da bi.

Ran 12 ga wata, an samu mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, a sa'i daya kuma, an ji girgizar kasa a larduna da birane da dama, a ciki har da Beijing da Shanghai da Gansu da Shanxi da kuma Shaanxi, haka kuma, an ji girgizar kasa a kasashen Viet Nam da Thailand. Ya zuwa ran 13 ga wata da karfe 7 da safe, mutane kusan dubu 10 sun rasa rayukansu a cikin girgizar kasar.(Tasallah)