Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, ya zuwa yau 13 ga wata da karfe 8 da safe, girgizar kasar da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, ta riga ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 10 da ke birni da larduna 8.
Da misalin karfe 2 da minti 28 na ran 12 ga wata da yamma, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Bayan aukuwar wannan girgizar kasa, ba tare da bata lokaci ba ne, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da muhimmin umurni, inda ya nemi da a ceci mutanen da suka jikkata tun da wuri domin tabbatar da lafiyar jama'ar da wannan bala'i ya rutsa da su. Sannan kuma an kafa ofishin ba da umunin fama da bala'in girgizar kasa da ke karkashin jagorancin firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin. Yanzu firayin minista Wen Jiabao yana lardin Sichuan, don jarorancin ayyukan fama da bala'in.
A ran 13 ga wata da safe, Wen Jiabao ya bayyan cewa, wannan girgizar kasa ita ce wani bala'i daga indallahi mafi tsanani, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen tattara mutane da kayayyaki domin tallafa wa yankuna masu fama da bala'in.
A ran nan kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudaden Sin wato Yuan miliyan 860 cikin gaggawa domin samar da taimako ga yankuna masu fama da bala'in wajen gudanar da ayyukan ceto.
Kuma firayim minista Wen Jiabao ya jaddada cewa, tilas ne za a kammala ayyukan shimfida hanyoyin zuwa yankunan da ke cibiyar girgizar kasa kafin ran 13 ga wata da karfe 12 da dare domin gudanar da ayyukan fama da girgizar kasa da ceton mutane daga dukkan fannoni.(Kande Gao)
|