Ran 13 ga wata, wasu gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya sun ci gaba da aikawa da talgiram zuwa ga shugaba Hu Jintao na kasar Sin da kuma firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin, ko kuma ba da sanarwa domin jajantawa kasar Sin bisa mummunar girgizar kasa a gundumar Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin.
Shugaba Dmitri Medvechev na kasar Rasha ya nuna tausayi sosai kan girgizar kasar a Sichuan, ya kuma nuna jaje cikin sahihanci ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu. Firayim ministan Putin na Rasha ya bayyana cewa, Rasha tana son ba da taimakon da ya wajaba wa jen yaki da girgizar kasa da ba da agaji
Shugaban kasar Romania da shugaban kasar Pakistan da firayim ministan Pakistan da shugaban kasar Laos da firayim ministan Laos da shugaban kasar Korea ta Kudu da sarkin kasar Jordan da shugabannin kasashen Italiya da Poland da Brazil da Mexico dukkansu sun nuna juyayi ga wadanda suka mutu a cikin girgizar kasa, sun kuma bayyana cewa, suna goyon bayan ayyukan yaki da girgizar kasa da ba da agaji da gwamnatin Sin da jama'ar Sin suke gudanarwa da. A sa'i daya kuma, ma'aikatan harkokin waje na kasashen Romania da Japan da Bhutan da Isra'ila da Argentina da Costarica da Colombia su ma sun nuna wa kasar Sin jaje.(Tasallah)
|