Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 15:08:34    
Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa lardin Sichuan, don jagorancin ayyukan fama da bala'in girgizar kasa

cri

Jiya 12 ga wata da yamma da karfe 2 da minti 28, an samu girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Wannan girgirzar kasa tana da karfi sosai, kuma ta shafi yankuna da yawa, a sakamakon haka, mutane da yawa suka rasa rayukansu ko ji rauni. A wannan rana da dare, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa birnin Du Jiangyan na lardin Sichuan da wannan bala'i ya rutsa da su, don soma jagorancin ayyukan fama da bala'in.

Mr. Wen Jiabao ya bukaci sojojin da suke aikin fama da bala'in da su kawar da dukkan matsaloli, don zuwa yankuna da suka fi fama da bala'i, har ma da kafa.

Bisa labarin da muka samu an ce, bayan faruwar wannan bala'in girgizar kasa, bangarori daban daban da abin ya shafa na kasar Sin sun aika da mutane masu aikin fama da bala'in, da kuma yi jigilar da kayayyaki zuwa yankuna masu fama da bala'in. Yanzu, sojoji da 'yan sanda na musamman kusan dubu 20 sun isa yankuna masu fama da bala'in, saura fiye dubu 10 kuma suna kan hanyar zuwan yankunan. Bayan haka kuma, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, da ma'aikatar kudi ta kasar, sun bayar da kudi cikin gaggawa da yawansu ya kai kudin Sin RMB miliyan 200 ga wuraren da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan, don bayar da taimako ga mutanen da ke yankuna masu fama da bala'in da su warware matsalar zaman rayuwarsu. Kazalika kuma, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta shirya tantuna 25000 ga yankuna masu fama da bala'in, yanzu kuma ana shirya da jigilar sauran kayayyakin fama da bala'in. (Bilkisu)