A ran 12 ga wata da dare, zaunanen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin wato jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar ya kira taro don shirya aikin ceton bala'in girgizar kasa daga duk fannoni.
Mahalartan taron sun saurari rahoton da hukumar da abinya shafa ta yi musu kan yanayin bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan dake lardin Sichuan. Taron ya jaddada cewa, dole ne, kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatocin wurin da hukumomin tsakiya da abin ya shafa su gaggauta daukar matakan ceton mutanen da suka ji rauni don tabbatar da lafiyar mutanen dake fama da bala'in a yankin, kuma za a yi iyakacin kokari wajen rage hasarar da bala'in girgizar kasa ya kawo musu.
Taron ya nemi gaggauta tura sojoji da masu aikin likita zuwa yankin dake fama da bala'in don ceton mutanen da suka ji rauni. Kuma ya kamata a yi sufurin abinci da ruwan sha da magunguna da tantuna da kuma sauran agaji. Bugu da kari, ya kamata a gaggauta gyara gine-gine da ayyukan da suka lalata a bala'in, a dudduba yanayin bala'in girgizar kasa ko-ta-kwana da daukar matakai masu amfani don magance sake aukuwar bala'in da abin ya shafa.(Lami)
|