Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 14:05:10    
Wasu gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa sun nuna jejeto ga kasar Sin domin bala'in girgizar kasa da ya faru a lardin Sichuan

cri

Bayan da girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter auku a ran 12 ga wata a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, wasu gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa sun nuna jejeto ga kasar Sin bi da bi.

A ran 12 ga wata, firaministan Japan Fukuda Yasuo da shugaban Rasha Dmitri Medvechev da shugaban kasar Amurka Bush da kuma shugabanni daga kasashen duniya sun aika da sakon jejeto zuwa ga shugaban kasar Sin Hu Jintao daya bayan daya, inda suka nuna juyayi ga bala'in girgizar kasa mai tsanani da ya auku a kasar Sin. Shugabanni da dama sun nuna cewa, suna son su samar da agaji ga yankunan dake fama da bala'in a kasar Sin.

A ran nan, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya buga waya ga ministan harkokin waje, a madadin MDD, ya nuna jejeto ga gwamnati da jama'ar kasar Sin. Ban Ki-Moon ya furta cewa, MDD za ta yi iyakacin kokari wajen nuna goyon baya ga ayyukan ceto da sake ginawa da kasar Sin ta yi.

Bugu da kari, a ran 12 ga wata, shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Rog ya aika wasika zuwa ga Mr. Hu Jintao don nuna juyayi ga mutanen da suka mutu a bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan. Mr. Rog ya ce, kwamitin wasannin Olympic na duniya yana son ya hada gwiwa sosai da jama'ar kasar Sin don tinkarar bala'in.

Ban da wadannan kuma, bi da bi ne, ma'aikatun harkokin waje na Faransa da Isra'ila da Turkey da Iran da Singapore da Argentina da kuma sauran kasashe da kwamitin kungiyar EU sun nuna gaisuwa da jejeto ga bala'in girgizar kasa da ya auku a kasar Sin.(Lami)